Akwai yiyuwar yau gwamnatin tarayya zata amince da mafi Ƙarancin albashi da kuma tattauna sauran matsalolin da suke addabar ƙasar.
A na tunanin batun albashi shi zai jagoranci zaman domin kwamitin da aka naɗa domin tattauna mafi ƙarancin albashi ya bada rahoton sa ga Shugaban ƙasa.