Akwai yiwuwar haɗarin ambaliya ya afka wa mutane miliyan 3.7 a Kano – NEMA

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar bada agaji ta gaggawa, NEMA ta yi gargaɗin cewa aƙalla mazauna sama da miliyan uku a yankuna 362 na ƙananan hukumomi 14 a jihar Kano ne ke cikin barazanar ambaliyar ruwa sama a daminam bana.

Rahotanni sun bayyana cewa, daga sati ɗaya zuwa yanzu an samu mamakon ruwan sama a Kano wanda hakan ya haifar da raguwar gudanar da ayyukan yau da kullum na al’umma a jihar.

Darakta Janar ta hukumar, Zubaida Umar ta faɗi hakan a lokacin wani taron ƙara wa juna sani da masu-ruwa-da-tsaki kan harkokin kula da shara da shirya wa ambaliya ta tare da ɗaukar matakan kariya gabannin aukuwar su.

Haka kuma, NEMA ta ce aƙalla mutane 227,494 ne a jihohin Nijeriya 27 lamarin ambaliyar ruwan sama ya shafa.

Ƙananan hukumomin da aka lissafo sune; Rimin Gado, Tofa, Kabo, Madobi, Garun Malam, Bebeji, Rano, Dawakin Kudu, Warawa, Wudil, Sumaila, Ajingi, Kura da kuma Dala.

Haka nan, Kwamishinar Ma’aikatar jinƙai da kawo ƙarshen talauci ta jihar Kano, Hajiya Amina Abdullahi ta jaddada ƙoƙarin gwamna Abba Kabir Yusuf na kula da kuma kiyaye al’ummar jihar daga aukuwar annoba da ibtila’i a faɗin jihar.

By Babaji