
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.
Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Katsina, Isa Muhammad Musa Ƙanƙara ya sanar da kawo ƙarshen matsalolin ruwan sha da wutar lantarki a jami’ar Umaru Musa Yar’adua.
Ya ce, tuni dai aka magance na ruwan bayan farfaɗo da rijistar burtsatse ga mutane a jami’ar.
Kwamishinan ya na amsa waɗannan tagwayen tambayoyin ne a wata hira da ya yi da manema labarai a ofisoshinsa da ke Katsina.
Ƙanƙara ya kara da cewa, ita kuma matsalar wutar lantarki, kamfanin samar da wutar lantarki (KEDCO) tare da haɗin gwiwar jami’ar su na cigaba da ƙoƙarin samar da isasshen wutar lantarki da kuma mai amfanin da hasken rana.
Ya ce, nan bada jimawa ba waɗannan matsaloli da ma wasu da suka adabi jami’ar zasu zama tarihi.
Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na inganta harkar ilimi a kowane mataki a faɗin jihar wanda jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta na ɗaya daga ciki.
Jami’ar dai ta na fuskantar waɗannan matsaloli wadanda suka kusa ɗurƙasar da harkokinta na yau da kullum a jihar Katsina.
