Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce, rikicin Masarautar Kano ya dame shi matuƙa gaya, amma ba ya son shiga cikinsa.
A wata hira da tsohon gwamnan, wanda aka nuna a gidan Talabijin na Channels a shirin Siyasa A Yau, ya ɗora laifin rikicin a kan ‘yan siyasa, yana fatan za a warware shi nan ba da jimawa ba.
Ya ce, “Ni babban memba ne a majalisar masarautu kuma baya ga haka na yi mulkin jihar.
“Don haka ni babban ɗan jihar ne. Ranar da maganar ta kai kotu, na ce ba zan yi magana ko tsoma baki a kan komai ba.
“Wannan ya dame ni. Ni ɗan Kano ne. Ina son komai na Kano ya zauna lafiya. Muna jira kuma addu’a ta ita ce mu shawo kan ta cikin gaggawa.
“Za a samu zaman lafiya. Muna buƙatar cibiyar gargajiya. Ba zan shiga hakan ba saboda ina cikin cibiyar.
“Saka siyasa a harkar masarauta ta kai mu cikin wannan rikicin. Idan da ’yan siyasa sun nisantar da duk wannan, to da babu shakka cibiyar gargajiya za ta zauna daram.
“Cibiyoyin gargajiya suna kan gaba a cikin al’umma. Gwamna ko duk wanda gwamnati ta naɗa shugaba ne. Dole ne a sami wannan haɗin kai na fahimta.
