Alaƙar jinin al’ada da zamantakewar aure

Daga AISHA ASAS

Allah S.W.A ya faɗa a cikin littafi mai tsarki “suna tambayar ka game da haila (al’ada) ka ce masu ƙazanta ne, su nisance mata har sai sun yi tsarki.”

A wannan ayar mata suke fakewa suka haramta ko sumbatar mazajensu. A cewar su ko hannu ya haramta miji ya riƙe na matar sa har sai ta yi tsarki.

Uwar gida ki sani a lokacin da ki ke al’ada saduwa kawai aka haramta maku. Da yawa mazaje masu mata ɗaya sukan shiga mawuyacin hali a lokacin da matansu ke al’ada wanda kaɗan ne daga cikinsu ke iya riƙe kansu.

A vangare ɗaya uwar gida ta ce, bata son kishiya, amma bata san yadda za ta gamsar da maigidanta a lokacin da take al’ada ba.

Na sani maza sun kasu daban-daban ta ɓangaren gamsuwa, wani komai zai samu idan ba a kai ƙarshe ba ba zai gamsu ba. Sai dai duk da haka yana da matuqar muhimmanci sanin hanyoyin kawar da sha’awa tsakanin ma’aurata. Domin za a iya samun kaso tamanin bisa ɗari na biyan buƙata ta hanyar. Hakan zai taimaka matuƙa a lokacin da ki ke al’ada.

Uwar gida ba jima’i kawai ne kwanciyar aure ba, ko ba lokacin da ki ke yin al’ada ba, yana da kyau ki kasance mai tunanin hanyoyin gamsar da maigida ta sauran gaɓoɓin jikinki. Hakan na ƙara danƙon soyayya da ƙarin sha’awa da marmarin aurattaya.

Jinin al’ada ba ya haramta wasa ta ma’aurata daga mataki na farko har na biyu ya halasta, na ukun kawai aka haramta.

Akwai wani kuskure da mata ke yi a lokacin jini, wanda ba zan iya cewa na san isnadinsa ba, sai dai na san ya jima yana yawo a tsakanin matan Hausawa, duk da cewa malamai sun fito, sun yaqe shi, hakan bai hana ya rayu har kawowa yau ba, ba komai nake magana kai ba, face ɗabi’a ta raba shimfiɗa da maigida yayin jinin al’ada.

Ba zan iya cewa dukka laifin a iya mata ya tsaya ba, domin akwai mazaje da yawa da ke ƙyamar mace yayin da jini ke mata zuba, duk da haka akan samu matan da ke da wannan ra’ayi, kuma suka tsayu kansa, koda kuwa mazajensu ba sa son hakan, watakila hakan na da nasaba da irin huɗubar iyayen da, a ƙoƙarin ganin miji bai kusanci matarsa a lokacin jini ba, sai a nuna mata qaurace shimfiɗarsa har sai ta yi wanka.

Wannan ba addini ba ne, domin an ruwaito cewa, Nana Aisha Allah Ya ƙara yarda da ita, ta kasance tana ɗaura zani daga cibiyarta zuwa gwiwa, kuma ta kwanta tare da Manzon rahma. Kuma idan kin kasance mata ɗaya a wurin mijinki zai iya shiga wani hali, musamman ma ga wadda take yin kwanaki masu yawa.

Idan mun tafi ga matsala ta gaba, wadda ta zama ruwan dare ga matan aure na wannan zamani, wato rashin sanin yadda matar aure zata tsaftace jikinta a lokacin da take yin jini. Idan na yi zancen tsafta ba wai na tsaya iya wanke kanfai ko ƙyalen al’ada ba. Zancena har ga sanin yadda za ki hana ƙarnin jinin bayyana a jikinki, da bayinki, sanin yadda za ki hana jinin zuba har ya yi tabo a tufafinki.

Abin takaici har yau akwai matan da ba su iya tsaftace kansu a lokacin da suke jini na al’ada, hakan ya sanya duk wata ya yi za a iya gane lokacin da suke yi ta hanyar rashin kulawar su. Wata macen idan ta sanya ƙyale ko kaxa sai jinin ya cika ta har ya taɓa zaninta kafin ta canza. Hakan zai sa a dinga ganin sirrin nata na ɓoye.

Yana da kyau uwar gida ta fahimci lokacin al’ada lokaci ne na buƙatar ƙarin tsafta sama da wadda ki ke yi a baya. Idan kina wanka sau ɗaya a rana to lokacin al’ada ya kamata ki mayar da shi biyu zuwa uku musamman a lokacin zafi, ko idan kin lura kina yawan zubar jini. Ki tabbatar ba mai jiyo ƙarnin jinin ta hanyar yawan canza ƙunzugin akai-akai da wanka lokaci-lokaci, yawan tsarki da ruwan ɗumi, tare da amfani da turare duk arhar shi.

Idan har ba ki da halin siyen kaɗa ta bature mai yawa da zata ishe ki canzawa lokaci-lokaci, to ki na da zavin amfani da ƙyale mai kyau wanda za ki iya wankewa ki ƙara sawa. Amma fa sai kin kula da tsaftace su yanda ya kamata.

Mata da yawa sun jahilci al’ada, ko ince ba su ɗauke ta a matsayin komai ba face ƙazanta hakan kan sa wasu har magani suke sha don ganin sun hana kansu jinin.

Tabbas ƙazanta ce, amma ba ma tunanin illar da ƙazantar zata iya yi mana idan bata samu damar fitowa ba, kowa dai ya san ƙazanta kyanta zubarwa.

Abin da matan da ke hana kansu jini ba su sani ba, al’ada wani nau’i ne na gyaran mace idan har kin bi tsari da dokoki zai zame maki kayan mata da za ki ji daɗin su. Sai dai ta yaya?

Bari mu yi a gwarance ba ilimince ba yanda kowa zai gane. Mazan da suke kula da kansu za ka same su su na ‘yan shaye-shayen kayan wankin mara don kawar da abin da zai hana su bajinta a auratayya. To me ya sa mata ba sa wannan ɓangaren na gyara? Duk da cewa kusan abin da maza ke ci ko sha su buƙaci wannan gyaran mata ma na cin su. Amsar dai ita ce, saboda suna al’ada. Ita ce ke tafiya da duk wata dattin mara da ta farji. Kenan a nan za mu iya kiran al’ada a matsayin magani ta wannan vangare.

A lokacin da ki ke al’ada akwai ababen da za ki iya riƙewa don samun ni’ima bayan kammalawa. Domin al’ada na tafiya da kaso sitin bisa ɗari na shaye-shayen kayan mata da muke yi don illarsu duk da cewa akwai alfanu a cikin waɗansu daga ciki.

Yana da kyau uwar gida ki ƙara zafin ruwan da ki ke tsarki da su a duk lokacin da ki ka fara al’ada. Uwar gida ki guji barin ƙyale ko kaɗa a jiki ya jima, domin jimawar na iya haifar da wasu curutta ciki har da warin gaba.

Uwar gida a duk lokacin da ki ka fara al’ada ki tanadi zuma mai kyau, ki zuba cokali uku na zumar a ruwan zafi tamkar dai za ki sha shayi, ki shanye. Za ki maimaita hakan a kowacce safiya har ƙarshen al’ada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *