Almundahana: Gwamnati ta naɗa muƙaddashin Akanta-Janar

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta amince da naɗin
Mr. Anamekwe Chukwunyere Nwabuoku a matsayin wanda zai ci gaba da riƙon ofishin Akanta-Janar na Tarayya biyo bayan binciken da EFCC ke kan gudanarwa kan Akanta-Janar, Ahmed Idris bisa zargin almundahana.

Hakan na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Sakataren Ma’aikatar Kuɗi da Tsare-tsare na Tarayya, Aliyu Ahmed ya sanya hannu mai ɗauke da kwanan wata 20 ga Mayu, 2022.

Wasiƙar ta ce naɗin zai yi aiki ne ya zuwa lokacin da bikin zai kammala.

Kafin wannan lokaci, Nwabuoku darakta ne a Ofishin Akanta-Janar, inda yanzu ya zama mai kula da ofishin na Akanta-Janar ɗin.

Mr. Anamekwe ya yi karatu mai zurfi kuma ya halarci tarurrukan sanin makamar aiki a lokuta da dama kuma a wurare daban-daban.