’Yan Nijeriya na shanye barasa da lemon kwalba na Naira biliyan 246 a wata uku – Rahoto

Daga AMINA YUSUF ALI

Rahotanni sun bayyana cewa, a cikin kowanne watanni uku ‘yan Nijeriya sukan kwankwaɗe barasa da lemunan kwalaba na wuri na gugar wuri har na sama da biliyan Naira 245.61.

Sakamakon wani rahoto mai taken Q1 2022 da aka gudanar a kan manyan rukunin kamfanonin samar da ababen sha guda uku wato, kamfanonin gida Nijeriya, kamfanonin wajen ƙasar nan da kuma kamfanin Guinness Nigeria ya bayyana cewa, yadda yawan masu yi wa kamfanonin ciniki yake ƙaruwa ya tilasta kamfanonin ƙara zagewa wajen ganin ababen shan ba su yanke wa masu saye ba. 

Wannan ba makawa shi ya ƙara bunƙasa ribar da kamfanonin suke samu a harkar lemon kwalaba da barasa. 

Rahotanni sun bayyana a ƙarshen shekarar da ta gabata kamfanonin sun samu ribar Naira biliyan N187.24 a matsayin kuɗin cinikin kayan nasu.