Hukumar ƙwallon ƙafar Ingila ta tuhumi ɗan wasan Chelsea, Mykhailo Mudryk da laifin karya ƙa’idojinta na hana amfani da ƙwayoyi masu ƙara kuzari, bayan da ya gaza tsallake gwajin ƙwayoyin.
Halin yanzu, ɗan wasan zai iya fuskantar hukuncin dakatar da shi na tsawon shekaru huɗu, hukumar FA ta dakatar da ɗan wasan na ƙasar Ukraine, mai shekara 24 na wani ɗan lokaci a cikin watan Disamba bayan fitowar sakamakon binciken da aka yi a gwajin fitsari.
Chelsea ta ƙulla yarjejeniya da Mudryk daga Shakhtar Donetsk a watan Janairun 2023 kan kudi har fam miliyan 89, kuma yana da kwantiragi a kungiyar har zuwa watan Yunin 2031, Mudryk ya zura ƙwallaye 10 a wasanni 73 da ya buga a dukkanin gasannin da ya buga wa Chelsea.
’Yan wasan da aka samu da amfani da ƙwayoyi masu ƙara kuzari da gangan ka iya fuskantar dakatarwa tsawon shekaru huɗu a ƙarƙashin jagorancin hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, Fifa, a lokacin gwajin Mudryk ya ce bai taɓa yin amfani da wasu haramtattun abubuwa da gangan ba, tun ranar 28 ga watan Nuwamba bai buga wa Chelsea wasa ba.
Murdyk ya halarci wasan ƙarshe na gasar cin kofin UEFA Conference League da Chelsea ta doke Real Betis a watan da ya gabata, amma kuma ba a cikin tawagar Chelsea ba, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, FA ta ce “Za mu iya tabbatar da cewa an tuhumi Mykhailo Mudryk da laifin keta dokar hana ƙara kuzari, ta hanyar amfani da wani abu da aka haramta, wanda kuma ya saɓa wa doka ta 3 da 4 a kundin dokokin FA na hana ƙara kuzari.
Zuwa yanzu Chelsea ba ta ce komai ba dangane da tuhumar da ake yi wa Murdyk amma a watan Disamba ta ce, ta na fatan ɗan wasan nata yayi nasara duba da cewa “Mykhailo ya tabbatar da cewa bai taba yin amfani da haramtattun abubuwa da gangan ba” ta ce a cikin sanarwar, a karkashin dokokin FA, ‘yan wasa sunada ’yancin bukatar ayi masu gwaji na biyu bayan an samu tabbacin amfani da ƙwayoyi masu ƙara kuzari a gwajin farko, amma idan gwajin na biyu ya zo daidai da na farko to za a yanke masu hukunci.
