Amurka na shirin bai wa jama’a damar kallon abubuwan da aka haramta

Spread the love

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na shirin ƙaddamar da wani sabon shafin intanet mai taken “Freedom.gov”, wanda manufarsa ita ce bai wa jama’a, musamman mazauna Turai damar shiga da kallon abubuwan da gwamnatocinsu suka takaita ko suka haramta.

Rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar ya nuna cewa shirin na ƙarƙashin jagorancin Mataimakiyar Sakataren Hulɗa da Jama’a ta Amurka, Sarah Rogers, kuma an yi niyyar sanar da shi a wani taron tsaro da aka gudanar a birnin Munich na Jamus, sai dai aka dakatar ba tare da bayyana dalili ba.

Majiyoyi sun ce an tattauna yiwuwar sanya wata fasaha da ke ɓoye asalin mai shiga shafin, ta yadda zai bayyana kamar daga cikin Amurka yake shiga, domin kauce wa takunkumin dokokin ƙasashen Turai.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Donald Trump ke mai da batun ’yancin faɗar albarkacin baki ginshiƙin manufofinta na ƙetare, tare da zargin Turai da murƙushe wasu ra’ayoyi a kafafen sadarwa.

Sai dai masana na ganin cewa wannan shiri zai iya zama tamkar ƙalubale kai tsaye ga dokokin Tarayyar Turai, musamman waɗanda ke taƙaita kalaman ƙiyayya da yaɗa bayanan ƙarya. Haka kuma, zai iya jefa Amurka cikin zargi na ƙarfafa karya dokokin ƙasashen da take hulɗa da su.

By ukarofi