Gwamnati Kanada ta fara shirin rage dogaro da Amurka a ɓangaren tsaro

Spread the love

Gwamnatin Kanada ta sanar da sabbin sauye-sauye a tsarin karɓar baƙin haure masu ƙwarewa, inda za a fara bai wa wasu rukunai na musamman fifiko domin cike giɓin ƙwararru a sassa masu muhimmanci.

Ministar Shige da Fice ta ƙasar ta ce sauye-sauyen na shekarar 2026 za su jawo ƙwararru da za su iya fara ba da gudunmawa nan take, musamman a ɓangaren kiwon lafiya, bincike, sufuri da kuma tsaro.

Firayim Minista Mark Carney ya jaddada cewa maƙasudin shirin shi ne rage yawan mazauna na dindindin da ake karɓa a ƙasar, tare da mayar da hankali kan hazikai da za su taimaka wa tattalin arziki da tsaro.

Sabbin rukunai sun haɗa da:

Likitoci da ma’aikatan jinya da ke da ƙwarewa a cikin Kanada, matuƙan jirgi da masu gyaran jiragen sama, manyan shugabannin kamfanoni, sojojin ƙwararru daga ƙasashen waje, ciki har da likitocin soja da matukan jiragen yaƙi

Masu nazari na ganin wannan mataki na nuna yadda Kanada ke neman gina ƙarfinta na cikin gida, musamman a lokacin da dangantakarta da Amurka ke fuskantar sabbin ƙalubale.

By ukarofi