Shugaban Jamus na goyon bayan taƙaita wa yara amfani da kafofin sadarwa 

Spread the love

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya bayyana goyon bayansa ga matakan da za su taƙaita damar yara shiga kafafen sada zumunta, yana mai cewa illar bayanan ƙarya da ake kirkira ta hanyar fasahar zamani ta sa ya sake duba matsayinsa.

Ya ce ba za a bar al’umma ta rushe sakamakon yaɗuwar bayanan bogi da aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a ba, musamman idan yara ne ke yawan shafe sa’o’i masu yawa a kan intanet.

Jam’iyyarsa ta nemi a hana yara ƙasa da shekara 16 shiga wasu manhajoji, yayin da ake sa ran jihohin ƙasar za su tattauna yadda za a kafa dokar da za ta shafi ƙasa baki ɗaya, ganin cewa tsarin Jamus na bai wa jihohi ikon tsara dokokin kafofin watsa labarai.

Masu ra’ayi sun ce matakin na daga cikin yunƙurin Turai na kare matasa daga illolin fasahar zamani, musamman bayan ƙasashe da dama sun fara ɗaukar irin wannan mataki.

By ukarofi