Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
A daidai lokacin da aka gab da fara muƙabal tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da malaman Kano, an bayyana sunayen malaman da zai fafata da su.
Malam da ake sa ran za su yi zaman muƙabala da Sheikh Jabbaru a yau Asabar, su haɗa da; Malam Abubakar Mai Madattai daga ɓangaren Tijjaniyya da Malam Kabir Bashir Ƙofar Wambai daga ɓangaren JIBWIS da Dr Rabi’u Umar Sani Rijiyar Lemo daga ɓangaren Salafiyya, sai kuma Malam Mas’ud Hotoro daga ɓangaren Ƙadiriyya.
Shugaban Jami’ar Istiƙama da ke Kano, Farfesa Salisu Shehu, shi ne alƙalin muƙabalar.




