Rayuwar ‘yan wasan kwaikwayo a Arewa daga Ibrahim Mandawari

Daga IBRAHIM MANDAWARI

Kamar yadda wasu suka sani wasan kwaikwayo a Arewacin Nijeriya ya samo asali ne tun lokacin Mulkin Mallaka, wato lokacin da Turawan Ingila ke mulkin wannan ƙasa tamu Nijeriya. Hakan kuwa ya samo asali ne daga fuskoki guda uku; wato:

Fuska ta ɗaya, wasannin kwaikwayo domin wayar da kai ga talakawa a fannoni daban-daban na rayuwa, misali wayar da kai a kan bunƙasa aikin gona musamman noman gyaɗa da auduga (Shirin Baban Larai), da kuma shiri a kan wayar da kai domin a ƙyale mata masu ciki su dinga halartar ƙananan asibitoci don haihuwa (Mama Learns a Lesson) da irin su fin ɗin ‘Amarya’ wanda aka yi shi a kan nuna illar yadda magidanta kan bar iyalinsu su tafi yawon bariki.

Fuska ta biyu kuwa, shi ne wasan kwaikwayo na daɓe irin wanda ‘yan makaranta kan yi domin wayar da kai kan muhimmancin ilimi, waɗannan wasanni an fi yin su a makarantun firamare da sakandare a lokacin Turawa da farkon samun mulkin kai.

Sai fuska ta uku, wato wasannin kwaikwayo a talabijin irin wanda aka fara yi bayan samun mulkin kai a Nijeriya, irin wannan wasanni su aka dinga gabatarwa tun wajajen 1967 a lokacin yalin basasar Nijeriya a gidan talabijin na RTK, wato Radio Television Kaduna, zuwa NTV Kano, Sokoto, Jos da sauransu.

‘Yan Wasan Kwaikwayo na Talabijin
Akasarin irin waɗannan ‘yan wasa da ke fitowa a ire-iren wannan wasanni sun haɗa da irin su; Halifa Baba Ahmad, Ƙasimu Yero, Mustafa Muhammad Danhaki, Alƙali Kuliya, Karƙuzu da sauransu. Sannan yawa-yawansu kuma sun faro ne tun suna ‘yan makaranta wasu kuma tun suna yara ƙanana.

Tafiya ta yi nisa har zuwa wajajen 1981 yayin da gwamnonin jam’iyyun adawa a jumhuriyya ta biyu suka haɗa kai suka kafa gidajen talabijin mallakar jihohinsu inda ƙungiyoyin wasannin kwaikwayo kuma suka ƙara samun damar gudanar da wasanni a waɗannan tashoshi. Daga nan ‘yan wasa suka sake kunno kai har wajajen 1988 zuwa 1990 inda aka shigo duniyar ‘Home Video’ domin kasuwantar da wasannin, waɗanda kuma daga baya ake kiransu Hausa films.

To, duka waɗannan jarumai ko ‘yan wasa sunayensu sun buwaya a ko’ina cikin duniya, amma fa haƙiƙanin rayuwarsu abar tausayi ce. Na iya tunawa a wani taron Hukumar s Daidaita Sahu ta jihar Kano a zamanin Gwamna Malam Shekarau, wata tsohowar ‘yar wasa ta miƙe ta ce ko atamfa ba ta taɓa saya da kuɗin da ake biyanta a wasan kwaikwayo ba. Haka ma a can shekarun baya, marigayi Alhaji Ƙasimu Yero ya taɓa yin wata hira a wata mujalla da ake bugawa a Kaduna yana mai cewa, “Babu wani kitse a wasan kwaikwayo.”

E, na san wasu ‘yan wasan talabijin a shekarun baya sun sami ɗan tallafi ko kulawa daga wasu gwamnatoci. Misali, Ƙungiyar Samanja Mazan fama sun samu kulawa a zamanin Janar Babangida, inda aka dinga ɗaukarsu a jiragen sama suna zuwa Fadar Shugaban Ƙasa suna gabatar da wasa, sannan aka mayar da shirin na su zuwa Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA Network).

Haka kuma tsohon Gwamnan Kano, Sata Kabiru Gaya, ya bai wa su Malam Mamman kujerar Hajji kowannensu. Can kuma Kwamishin Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna a wancan lokaci, Muhammadu Rabi’u Baƙo, ya bai wa Ƙasimu Yero muƙamin Shugaban Cibiyar Raya Al’adu ta Jihar Kaduna (Kaduns State Council For Art and Culture) da kuma ɗan tallafin da ‘yan wasa na talabijin suka riƙa samu nan da can.

Jaruman ‘Home video’ na farko kuwa irin su Hauwa Ali Dodo da Yusuf Barau da Ibrahim Mandawari da Waziri Zayyanu da Goloɓo da sauransu, sun fara samun kuɗi da sana’ar wasan kwaikwayo na ɗan lokaci, amma ƙalubalen zamani ya yi tafiyar yaji da akasarinsu, hasali ma ƙalilan daga cikinsu suka tsira da ‘yar motar shiga da gidan kwana, amma har yanzu na san akwai waɗanda ko gidan kwana ba su mallaka ba.

To yanzu tafiya ta yi nisa , wasu jaruman sun yi kuɗi, wasu sun samu rufin asiri, wasu kuma suna nan jiya i yau. Amma waɗanda za a iya cewa sun yi kuɗi su ne jaruman da suke hulɗa da ‘yan siyasa wanda suke ɗaukar tallar ‘yan takara, sai waɗanda suke hulɗa da manyan kamfanoni inda sukan yi musu tallace-tallace a kan allunan ‘billboard’ da talabijin da sauransu (Ambassadorship). Sai kuma rukuni na uku, su ne waɗanda sukan halarci manyan bukukuwan aure domin yin waƙoƙi salon ‘ga ni ga ka’ (stage performance).

To, amma fa waɗannan rukunan ‘Yan wasa guda uku su ne ƙalilan daga cikin ma su sana’ar wasan kwaikwayo (Jarumai) domin ko a ƙiyasi ba za su wuce kashi 20 cikin 100 ba, ke nan kashi 80 su ne ‘yan hannu baka hannu ƙwarya.

Na yi wannan nazari ne saboda yadda na ga akasarin lokuta idan jarumin fim ya samu kansa a halin rashin lafiya, ko wani ibtila’i na rayuwa, to an dinga yawo da ƙoƙon bara ke nan ana nema masa taimako.

To Ina Mafita?
Kafin na faɗi mafita, ina so in waiwayi ire-iren tallafi da ake gudanarwa ga ‘yan’uwa ma’abota wannan sana’a, waɗanda suka samu kansu a halin rashin lafiya ko haɗari ko kuma dai wata jarrabawa daga Allah.

Dole in fara yaba wa ‘Kannywood Vanguard’, wato majalisar tattaunawa ta ma su sana’ar shirya fina-finan Hausa wanda a ko yaushe mambobinta ba sa gazawa wajen kai agajin gaggawa ga ma’abota sana’ar waɗanda suka samu kansu a halin ƙaƙa-ni-ka-yi. Sannan akwai ɗaiɗaikun jarumai irin su Adam A. Zango da Rahma Sadau da Hadiza Gabon da ire-iren matasan jarumai waɗanda kan tallafa wa mabuƙata a ciki da wajen ‘Industry’.

Saura da me? Anya a Haka za a Tsaya? Zai yi kyau manyan ƙungiyoyin ma su shirya fina-finai, su kafa wani ƙaƙƙarfan kwamiti domin samar da asusun dindindin tare da samar da manufa da kuma hanyoyin samun kuɗaɗe daga ciki da wajen Kannywood da kuma ayyana irin tallafin da za a dinga bayarwa ga mabuƙata.

Na kiyaye wani tsohon jarumin fina-finan India, wato Arbela Mastana, ya dinga samun alawus duk wata daga Kungiyar Jarumai ta India. To, a nan ba wai za a maida hankali kan tsaffin ‘yan wasa ne kawai ba, a’a, ina nufin mabuƙata ko waɗanda suka sami kansu a halin ƙaƙa-ni-ka-yi.

Sannan wancan batun Shirin Inshora da aka samu a zamanin tsohon shugaban ƙungiyar MOPPAN, Abdullahi Maikano, zai yi kyau a waiwayi wannan tsari.

Sannan in da hali a kafa gidauniya a gayyaci dukkan manyan ‘yan siyasar Arewacin ƙasar nan da sauran attajirai domin su zuba gudunmawa mai kauri ta inda za a tashi da ‘gear one’.

Ibrahim Muhammad Mandawari shine Mai Unguwar Mandawari kuma babban jarumi a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *