An cafke matashin da ya yi garkuwa da ɗan shekara 3 ya binne shi da ransa a Katsina

Daga BASHIR ISAH

‘Yan sanda a Jihar Katsina sun cafke matashin da ake zargi da yin garkuwa da wani yaro ɗan shekara uku tare da binne yaron da ransa.

Mai garkuwar ya kashe yaron ne bayan kuma ya karɓi fansar N800,000 daga hannun mahaifin yaron.

‘Yan sandan sun ce an damƙe Abubakar Abdul-Aziz ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe uku na rana.

Matashin mazaunin Sabuwar Santa Quarters ne da ke cikin Ƙaramar Hukumar Musawa a jihar.

Cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin, Kakakin ‘yan sandan Katsina, Gambo Isah, ya ce wanda ake zargin ya shiga gidan wani mai suna Adamu Alhassan a ƙauyen Bacirawa ta haramtacciyar hanya tare da sace yaro ɗan shekara uku zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Ya ci gaba da cewa, ɓarawon ya ajiye wata wasiƙamai ɗauke da lambar waya a gidan inda ya buƙaci baban yaron, Adamu Alhassan, ya biya fansar N800,000.

Ya ce baban yaron ya kira waya kamar yadda aka buƙace shi tare da neman a yi masa sauƙi ya biya N150,000 don a sako masa ɗansa.

Ya ce bayan da ‘yan sanda suka samu rahoton batun nan take aka tura jami’ai suka shiga bincike inda a ƙarshe suka kamo Abubakar Abdulaziz.

Kakakin ya ce yayin binciken ‘yan sanda, wanda ake zargin ya yi iƙirarin aikata laifin, tare da cewa ya binne yaron da ransa bayan ya karɓi kuɗin fansar. Bincike nana ci gaba da gudana in ji jami’in.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *