Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Kansiloli bakwai daga cikin 11 da ke akwai a Karamar Hukumar Argungu da ke Jihar Kebbi sun tsige Hon Samaila Muhammad Felande, kansila mai wakiltar Mazabar Felande daga mukaminsa na Shugaban Kansiloli, wato Council Leader, bisa ga zargin rashin tabuka wani abin a-zo-a-gani wajen jagoranacin kansilolin.
Kansila mai wakiltar mazabar Tungar Zazzagawa, Hon. Buhari Usman, ne ya bayyana haka jiya a garin Argungu bayan wani zama da suka yi.
Ya bayyana cewa, daga cikin korafe-korafensu akwai shirya wani gangamin taro a gidan Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar, Tafidan Kabi, da ke garin Argungu, wanda suka nemi ya yi musu cikakken bayanin makasudin gangamin kusan sama da wata daya, amma ya ki.
Bayan wannan kuma an gayyace shi su kansiloli biyu da Shugaban Karamar Hukumar Mulki ta Argungu Honarabul Salihu Ahmed KC ya rikewa albashi na watanni da kuma danne wa wadansu hakkokinsu.
Akwai sakaci na rashin tunkarar shugaban karamar hukumar mulki wajen kare mutuncinsu da kimarsu amma duk ya kawar da kai aka hada baki da shi ana danne hakkokansu da na sauran al’umma.
“Wadannan kadan ne daga cikin abubuwan da suka sanya muna ganin ba mu ya ke wakilta ba saboda haka shugabancinsa ba ya da amfani muka yanke shawarar tsige shi. Mu fa muna wakiltar mazabunmu ne da zummar kawo ci gaba ba don amfanin kawunanmu ba kadai,” in ji shi.
A bangaren wanda aka tsige, Honarabul Samaila Muhammad Felande ya bayyana cewa ya dai ga takardar tana yawo kafafen sada zumunta, sannan kuma shi wannan tsigewar bai yarda da ita ba saboda mutane biyar kacal ya gani kuma wanda ya saba wa doka, kansiloli goma sha daya ne ke akwai a karamar hukumar mulki ta Argungu saboda haka mutane biyar ba su isa su cire wani ba.
Ya kara da cewa maganar ya shirya wani gangami a gidan maigirma mataimakin gwamna ba gaskiya ba ne shi bai taba shirya wani gangami ba, haka-zalika bai sami wata takardar sanarwar gayyata ba ko daga bakin wani ko kuma a rubuce illa dai kawai wadannan mutanen suna yi wa shugaban qaramar hukumar mulki ta Argungu Honarabul Salihu Ahmed KC wata bita-da-kulli ne don su dadadawa masu gidajensu da ba su da shiri da shi rai.
