Fiye da mutum 50,000 ke zaman jiran shari’a a gidajen kurkukun Nijeriya – Jami’i

Spread the love

 Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An bayyana cewa akwai sama da mutum 50,000 tsare a kurkuku daban-daban cikin kasar nan, wadanda ke zaman tsammanin jiran a yanke masu hukunci a kotuna daban-daban.

Wani jami’i ne ya tabbatar da haka, inda ya ce kashi 69 bisa 100 na wadanda ke tsare a gidajen kurkuku, duk jiran a yanke masu hukunci suke yi.

Hukumar Kula da Gidajen Kurkukun Nijeriya (NCoS), ta ce akwai mutum 53,836 tsare a gidajen kurkuku daban-daban, wadanda ke zaman jiran a yanke masu hukunci a gidajen kurkuku 253 da ke cikin kasar nan.

Wannan kididdiga dai za ta iya karuwa, domin an yi lissafin adadinsu ne iyar ranar 18 ga Disamba.

Kakakin Yada Labarai na Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Kasa, Abubakar Umar ne ya bayyana haka, yayin ganawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ranar Alhamis, a Abuja.

Umar ce takaitaccen lissafin adadin masu jiran yanke hukuncin da wadanda aka yanke wa, su 77,849 ne a fadin kasar nan.

Ya ce wadanda aka yanke wa hukunci su 24,013 ne, tare da yin kari da cewa maza wadanda aka yanke wa hukuncin zama gidan kurkuku su 23,569 ne, mata kuwa 444.

Ya ce kididdiga ta nuna kashi 69 bisa 100 na wadanda ke tsare gidajen kurkuku, duk yanke hukunci su ke jira, sauran kashi 31 ne aka yanke wa hukunci,” inji shi.

Umar ya ce babban abin da ya fi damun gidajen kurkuku a kasar nan ita ce yawan cinkoson daurarru a gidan kurkuku, wanda cikin matsalolin da ke haddasa hakan, har da rashin dakunan aniyar masu laifi wadatattu kuma na zamani.

Ya ce yawancin dakunan duk tsoffin gini ne, kuma sun yi kadan.

Ya bayyana cewa gwamnatin Tarayya ta kara gina dakuna 3,000 a gidajen kurkuku daban-daban, ciki har da Kano, yayin da dakunan kurkukun Abuja da Fatakwal ana kan aikin su, an ma kusa kammalawa.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta fitar da Naira miliyan 585 domin biyan tarar da kotuna suka yanka wa wasu daurarru. Ya ce ta haka za mu samu saukin cinkoso sosai, idan aka saki wadanda ke zaman kasa biyan tarar da kotu ta aza masu.

Ya kuma jinjina wa kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi domin sakin daurarru 4,068.

By Editor