Nigeria Air: Majalisa ta gayyaci tsohon Ministan Sufurin Jirage – Sirika

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin sufurin jiragen sama da ya gayyaci Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, domin ya yi ma ta bayanin halin da kamfanin dakon kaya na kasa, Nigeria Air, ke shirin yi, har zuwa lokacin da zai bar mulki. Ana sa ran tsohon ministan zai bayar da haske a kan batutuwa da dama da suka shafi aikin.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Hon. Tarkighir Dickson ya gabatar a zauren majalisar ranar Alhamis.
Da yake gabatar da kudirin, ya ce tsohon ministan a shekarar 2016 ya ba da shawarar taswirar jiragen sama tare da kamfanin sufurin jiragen sama na kasa a matsayin aikin sa hannu, kuma ya yi alqawarin aiwatar da aikin kafin karshen gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar xan majalisar, tsohuwar ministan ya tunkari kamfanin jiragen saman qasar Habasha kwanaki kaxan kafin miqa jirgin domin samar da jirgin da za a iya samarwa ’yan Nijeriya a matsayin jirgin na ‘Nigeria Air’. Ya qara da cewa, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Nijeriya ta bayar da lasisin jigilar jiragen sama zuwa na ‘Nigeria Air’.

Dickson ya kara da cewa, “Gwamnatin da ta shude ta kashe biliyoyin nairori kamar yadda aka ce ta sayi sabon kamfanin jigilar kaya na kasa amma har yanzu ba a san matsayin aikin ba, ba tare da la’akari da biliyoyin kudaden masu biyan haraji da aka yi amfani da su wajen aikin ba.

“Idan ba a bincika mummunan halin da ake ciki ba, zai iya haifar al’amura tare da yin la’akari da cigaba da zama bazarana a cikin kasafin kudin tarayya.”

Majalisar ta amince da kudirin ta kuma umurci kwamitin da ya kuma gayyaci hukumar NCAA domin yi masa bayani kan aikin jirgin Nigeria Air da kuma tantance shi.

A watan Satumba ne ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo, ya dakatar da aikin jirgin Nigeria Air da kuma shirin bayar da wasu filayen saukar jiragen sama.

By Editor