Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A jiya Alhamis ne Kotun Koli ta jingine ranar yanke hukunci kan qarar da Jam’iyyar NNPP ta shigar ta na neman ta tabbatar da dan nasarar dan takararta, Abba Kabir Yusuf, a matsayin gwamnan Jihar Kano.
A watan Satumba ne dai kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Kano ta kori Yusuf a matsayin gwamnan jihar. Daga bisani, NNPP da dan takararta suka kalubalanci hukuncin a Kotun Daukaka Kara.
A ranar 17 ga Nuwamba, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin Kotun Kararrakin Zabe, sannan ta kara da cewa Yusuf ba dan Jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin da ya tsaya takarar.
Cece-kuce ya biyo bayan hukuncin kwanaki kaxan bayan da kundin hukuncin shari’ar na kotun daukaka qarar ya bayyana, wanda wasu sassansa suka saba wa hukuncin na ranar 17 ga Nuwamba.
Daga nan sai NNPP ta daukaka kara a gaban kotun koli, inda ta nemi a soke hukuncin kotun daukaka karar.
A daya bangaren kuma Jam’iyyar APC ta shigar da kara a Kotun Koli, inda ta kalubalanci kotun da ta ki amincewa da cewa Yusuf ya mika takardar shaidar jabu ga hukumar zabe ta kasa (INEC).
Kotun Kolin ta ce za a sanar da ranar da za a yanke hukunci ga dukkan bangarorin.
