An fara gasar Firimiya ta Ukraine yayin da ake ci gaba da yaƙi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumomin ƙasar sun haramta taruwar mutane a wuri guda, gudun kada Rasha ta harbo maikaman roka, hakan ya sa aka hana ‘yan kallo shiga filayen wasanni.

An buɗe gasar ƙwallon ƙafa ta Premier a Ukraine yayin da ƙasar ke ci gaba da gwabza yaƙi da Rasha.

A ranar Talata aka buɗe gasar ta 2022, amma an haramtwa masu kallo zuwa filayen wasanni.

Wasan farko an buga ne a filin wasa na Kyiv mai ɗaukar mutum dubu 65 tsakanin Shaktar Donetsk da Metalist 1925, inda aka ta shi canjaras.

Ƙasar ta Ukraine na ƙarƙashin matakin soji na ko-ta-kwana, inda aka haramta taruwar jama’a a wuri guda, gudun kada Rasha ta harbo makaman roka.

Hakan na faruwa ne yayin da ƙasar ke shirin gudanar da bikin samun ’yancin kai a ranar Laraba.

An ga ’yan sanda a tsaye a bakin ƙofar shiga filin wasa, wanda ciyayi ya rufe wani sassanta sanadiyyar rufewa da aka yi watanni shida da suka gabata, amma babu ɗan kallo ko ɗaya a cikin filin wasa.