Ina firgita idan na kalli teburin Firimiya – Klopp

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya ce, teburin gasar Firimiyar Ingila babu daɗin kallo a yanzu, bayan da ƙungiyar tasa ta rikito zuwa matsayi na 16 sakamakon shan kaye a hannun Manchester United da ƙwallaye 2 da 1 ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Har zuwa yanzu Liverpool ba ta samu nasara a ko da wasa guda daga cikin 3 da ta doka ba, a wasannin sabuwar kakar gasar ta Firimiya da aka faro, yayin da yanzu haka ta ke da tazarar mai 7 tsakaninta da Arsenal wadda ke jagorancin teburi.

Duk da cewa yanzu aka faro kakar ta bana, amma an jima rabon da aga Liverpool a irin wannan mataki bayan doka wasanni 3, ko da ya ke har yanzu ta na saman ƙungiyoyin da suka ƙunshi Everton da Wolves da Leicester da West Ham United a teburin na gasar Firimiya.

Da aka tambayi Klopp ko kawar da kai daga kallon teburin gasar Firimiyar Ingila zai amfanar, sai ya kada baki ya ce, idan kana so hankalinka ya tashi, to ka kalli teburin.