Ranar HAUSA: Lokaci ne na tunawa da harshe da adabi da al’adun Hausawa – Farfesa Ibrahim Malumfashi

“Bikin Ranar Hausa zai sa wa ‘yan gida da baƙi shauƙi da sha’awar harshen”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Farfesa Ibrahim Malumfashi fitaccen malami ne kuma masani a harshen Hausa da harkokin adabi, Marubuci, manazarci, ɗan jarida, masanin tarihi da rubuce rubucen mata a ɓangaren adabi, wasan kwaikwayo da tarihin gudunmawar marubuta a harshen Hausa. Duk wani wanda ya kwana ya tashi a fannin nazarin harshen Hausa da rubutun adabi a cikin Nijeriya da ƙasashen waje, babu shakka ya sallama wa Farfesa Ibrahim Malumfashi, saboda ɗimbin sanin da Allah ya bashi da a kan rayuwar Hausawa da harshen Hausa da kuma gudunmawar da yake kan ci gaba da bayarwa a wannan ɓangare. A yayin da manazarta da masu kishin cigaban harshen Hausa a ko’ina a faɗin duniya ke bukin wannan rana ta yau a matsayin Ranar Hausa, wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya samu zantawa da wannan shaihun malami, don sanin muhimmancin da bukin ranar ke da shi ga rayuwar miliyoyin Hausawa da masu nazarin harshen Hausa. A yi karatu lafiya.

MANHAJA: Yallaɓai, ko za ka gabatar mana da kanka?
FARFESA MALUMFASHI: Sunana Ibrahim Malumfashi. Farfesa ne na adabi a Jami’ar Jihar Kaduna. Ni manazarci ne kuma ɗan jarida da ke rubuce-rubuce a jaridu da kafafen sadarwa daban-daban.

A matsayin ka na Farfesa a harshen Hausa, wacce gudunmawa ka ke bayarwa kawo yanzu a ɓangaren haɓaka harshen Hausa?
Shekarata yanzu 35 ina koyo da bincike da karantar da adabin Hausa a jami’o’in Usmanu Ɗanfodiyo a Sakkwato da Umaru Musa Yar’adua a Katsina. Yanzu haka Ina koyarwa ne a Jami’ar Jihar Kaduna.

A cikin shekarun nan na yaye ɗaruruwan ɗalibai a matakin digiri na ɗaya da na biyu da na uku. Na kuma gabatar da maƙalu da bincike masu tarin yawa a gaban masana da kuma waɗanda aka buga mujallun ilimi a duk faɗin duniya.
Na rubuta littattafai guda 6 na adabi da tarihi da fassara kan rayuwar Hausawa.

Mene ne ra’ayinka game da bukin Ranar Hausa da aka ƙirkiro da ita?
Lokaci ne na tunawa da harshe da adabi da al’adun Hausawa, wanda kuma yana sa al’ummar duniya su fuskanci lamurran Hausa da Hausawa da yadda za a magance matsaloli da kuma ciyar da harshen Hausa gaba. Rana ce mai muhimmanci da zan so in ga an tabbatar da bukinta a kowacce shekara.

Mene ne tarihin kafuwar wannan rana?
Rana ce da waɗansu matasa suka haɗu suka samar da ita ƙarƙashin jagorancin ɗan jarida Abdulbaƙi Jari, ina jin shekara 6 zuwa 7 ke nan, domin tunawa da harshen Hausa da rayuwar Hausawa

Wanne cigaba irin wannan buki zai kawo wa harshen Hausa da Hausawa?
Al’ummar duniya za su tuna da harshen da mutanen da ke tu’ammali da shi ta fannoni daban-daban. Wannan biki na Ranar Hausa zai sa wa ‘yan gida da baƙi shauƙi da sha’awar harshe da adabi da kuma al’adun Hausawa.

Zai sa mutanen da ba su san da harshen ba ko ba su damu da shi ba, su gane ba ƙaramin harshe ba ne da irin darajar da Allah ya yi masa, za su kuma yaba da shi.

Yaya ka ke ganin matasa da sauran masu faɗa a ji za su taimaka a inganta wannan rana, ta yadda za ta kawo wa Hausawa sauyi da cigaba?
Tun da bikin ana yin sa ko’ina a faɗin duniya ta soshiyal midiya da kuma a zahiri, ya dace kowa da kowa a haɗa ƙarfi da ƙarfe a ga an tabbatar da faruwar wannan biki kowayce shekara, a kuma karɓi bikin da hannu bibbiyu ana kuma kawo sababbin take kowacce shekara domin ci gaban bikin.

Farfesa Ibrahim Malumfashi

Yaya ka ke ganin dacewar taken bukin ranar na bana, Muhimmancin Zaman Lafiya ga Al’umma?
Ƙwarai taken ya dace, musamman ganin halin da ake ciki yanzu na rashin tsaro da aukuwar ta’addanci da kidinafin da sace-sace. Taken zai ba da dama ga al’umma ta mayar da hankali kan waɗannan matsaloli da yadda za a kawar da su bakiɗaya.

Shin akwai wasu tarukan ko bukukuwa da aka shirya don raya wannan rana ta bana?
Da yake bikin a buɗe yake kowa da yadda zai gudanar da shi. Wasu a gidajen rediyo, wasu a jaridu, wasu a ɗakunan tarurruka a jami’o’in ƙasa bakiɗaya.

Mun gode ƙwarai da samun lokacin ka.
Na gode ni ma.