Gwamnatina za ta mayar da hankali wajen haɗin kan ƙasa – Atiku

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bada shawarar kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa domin tunkara da kuma magance matsalolin da suke addabar ƙasar nan.

Hakan na a ƙunshe ne a cikin bayanin da mataimaki na musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yaɗa labarai Abdulrasheed Shehu ya fitar.

Da yake jawabinsa, akan maudu’in miƙa mulki a Nijeriya cikin ƙarni na 21 a taron na Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa NBA karo na 62 a Birnin Ikko, wanda babban lauya Olisa Agbakoba ya jagoranta, Wazirin Adamawa ya koka game da taɓarɓarewar al’amura a Nijeriya da kuma alƙaluman bayanai marasa daɗi kan ƙasar, tun daga matsalar rarrabuwar kawuna da rashin tsaro da rashin aikin yi da fatara da sauransu, inda ya ce abu mafi muhimmanci shi ne yadda za a magance waɗannan matsalolin.

Ya ce tarihi zai so mu haɗa hannu mu yi aiki tare domin ceto Nijeriya, kuma damar yin hakan ta sake samuwa yanzu. Ya ce halin taɓarɓarewar da Nijeriya ta tsinci kanta yanzu yana buƙatar mutum mai ƙwarewa ya karvi ƙasar domin kuɓutar da ita daga durƙushewa.

Haka kuma, Atiku Abubakar ya ce yana da ƙwarewar da ake buata a shugabanci kasancewarsa cikin gwagwarmayar dimukuraɗiyya a ƙasar nan tsawon lokaci.

Ya kuma faɗi ɓangarori biyar dake buƙatar kulawa da suka haɗa da haɗin kan ƙasa da tsaro da tattalin arziki da rarraba iko tsakanin turakun gwamnati da kuma ilimi.

Ya jaddada cewar haɗin kan ƙasa zai samu ne ta hanyar tafiya tare da dukkan sassan ƙasar nan ta hanyar samar da gwamnatin haɗin kan ƙasa da sake fasalin ƙasar domin ƙara ƙarfin iko ga shiyyoyi sannan ƙananan hukumomi za su rage dogara da gwamnatin tsakiya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya gode wa waɗanda suka shirya taron saboda gayyatarsa da suka yi.

Taron wannan shekarar na NBA ya sami halartar manyan mutane a ɓangaren shari’a sannan kuma ‘yan takarar shugaban ƙasa sun halarci taron idan banda na APC.