An kama jami’in gwamnatin Nijar ɗauke da hodar iblis

Daga WAKILINMU

Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Agadas da ke arewacin Jamhuriyar Nijar ta tsare shugaban Ƙaramar Hukumar Fashi tare da direbansa bayan da ta gano kilogram fiye da 200 na hodar ibilis a cikin motarsa a ranar Lahadin makon jiya a wani wurin binciken jami’an tsaro.

Wasu shaidu sun ce, sunga jami’an hukumar na binciken wasu motoci ƙirar Toyota 4×4 da suka nuna matuqar shakku kan kayayakin da suke ɗauke da su, duk da dagewar wani mai muƙamin kansila da ya so ya kawo tarnaƙi a aikin jami’an da ke binciken.

Bayan kusa da sa’a ɗaya, jami’an hukumar suka tabbatar da abin da suke zargi, wato wasu harantattun abubuwan da aka saka a cikin manyan akwatina waɗanda aka yi amfani da motar iko wajan jigilar su.

An dai ƙiyasta cewa, darajar ƙwayar ta kai biliyan 5 na kuɗin CFA. Ya zuwa yanzu hukumomin’ ‘yan sanda na tsare da Sharou Sanda, shugaban Karamar Hukumar Fachi tare da matuƙinsa, yayin da ake ci gaba da neman wani mutun guda da ya haɗa baki da su, mutunen da bayanai ke nuna cewar kodawanne lokaci za a iya tasa ƙeyarsu zuwa birnin Yamai.

Ko a ranar 7 ga watan Disamban, 2021, sai da Hukumar Yaƙi da Sha da kuma Ta’ammuli da muggan ƙwayoyi ta yi kamen aƙalla kilogram 330 na wiwi tare da tsare mutum 10.

Tun bayan faɗuwar mulkin tsofon shugaban Ƙasar Libiya Mouammar Khadafi, wani ɓangare na Saharar Agadas da ke arewacin Jamhuriya Nijar ya zama wani yankin da masu fataucin muggan ƙwayoyi da makamai ke cin karansu ba babbaka duk da ƙoƙarin hukumomin ƙasar na tabbatar da tsaro a wannan yankin wanda ya raba iyaka da ƙasashen Libiya da Algeria da kuma Chadi.