Kyakkyawan fatan ganin sauyi cikin sabuwar shekarar 2022

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A cikin jawabinsa na sabuwar shekara ga ’yan Nijeriya, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sake tabbatar wa da jama’ar ƙasa cewa shekarar da ta gabata ba shekara ce mai daɗi ba ga kowa, saboda ƙunci da wahalhalun rayuwa da aka fuskanta. Sai dai kuma cikin jawabin nasa har wa yau ya ƙarfafa gwiwar ’yan Nijeriya da cewa, juriya, haƙuri da jajircewa su ne za su fitar da ƙasar nan daga halin da take ciki.

Ko da yake za a ce wannan jawabi na shugaban ƙasa ba jawabi ba ne na albishir, sai dai jawabi ne da za a iya cewa na ƙarfafa gwiwa, ga jama’ar ƙasa don a ƙara juriya da nuna kyakkyawan fata na ganin an samu ingantaccen sauyi a nan kusa. Ko da a jawabin sa na ranar sanya hannu a kan kasafin kuɗin wannan shekara, shugaba Buhari ya sake nanata ƙoƙarin da yake yi na ganin ya inganta rayuwar ’yan Nijeriya, kamar yadda ya yi alƙawari tun da farko.

Wasu ’yan Nijeriya da na samu damar zantawa da su sun bayyana ƙwarin gwiwar su na ganin wannan shekara ta zamo alheri, kuma ta zamo waraka daga abubuwan baƙin ciki da ƙunci da aka riƙa fuskanta cikin shekarar da ta gabata. Babu shakka wannan na nuna irin raɗaɗin da ’yan Nijeriya suka shiga, da ba wanda yake son sake ganin an sake maimaita halin da aka shiga.

Abin farin ciki ne da gwamnatin tarayya ta sanar da buɗe iyakokin ƙasa, domin ba da dama a shigo da wasu kayayyaki da dokar ƙasa ba ta haramta su ba. Fatan da ’yan Nijeriya suke yi shi ne, Allah ya sa hakan da aka yi ya zama mabuɗin samun sauƙin farashin kayan masarufi a kasuwanni da buɗewar harkokin kasuwanci waɗanda a baya suka kulle sakamakon rufe iyakoki da aka yi.

Har wa yau, ’yan Nijeriya da dama na farin ciki da ganin irin nasarorin da rundunonin tsaron ƙasa ke samu a kan ’yan ta’addan Boko Haram da ’yan ta’addan daji da ke haddasa kasha-kashe, kai hare hare, da satar mutane da dukiyoyi. Wannan babbar nasara ce ainun, ba ma kawai ga al’ummar yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma ba, har ma da sauran ’yan Nijeriya waɗanda ke bin manyan hanyoyin ƙasar nan zuwa wasu yankuna, domin harkokin su na kasuwanci da rayuwa. Amma suke faɗawa cikin haɗari, da shiga hannun ’yan bindiga, da ke kama su su yi garkuwa da su, don neman kuɗin fansa.

Lallai ’yan Nijeriya na burin ganin ƙarshen su Bello Turji da tawagar sa, da duk wasu masu aikata ɗanyen aiki irin nasu. A tsaftace hanyoyin ƙasar nan, ƙauyuka da dazuka daga sharrin ’yan ta’adda da sunan addini da masu ta’addanci don cin ribar rayuwa. ’Yan Nijeriya sun yi haƙuri sosai kuma sun nuna dauriya, daga wulaƙanci da ƙuntatawar da waɗannan ’yan bindiga ke haddasa musu. Tun kafin kowa ya fara ɗaukar mataki, don kare kawunansu da iyalan su.

Ƙarin kuɗin albashi da gwamnati ta ce ta yi wa jami’an ’yan sanda a ƙarshen shekarar da ta gabata, shi ma abin a yaba ne, domin hakan zai ƙara musu ƙwarin gwiwar gudanar da ayyukan su na samar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma. Ko da yake kamar yadda na jiyo wasu na faɗa shi ne ƙarin albashin bai taka kara ya karya ba, amma ko babu komai za a yabawa wannan gwamnati bisa yadda take ƙoƙarin kula da walwalar ma’aikatan ta, duk da yake dai tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi ta sa darajar albashin tana faɗuwa ƙasa sosai.

Ma’aikata da dama na samun kansu cikin wani mawuyacin yanayi na rashin sanin yadda za su yi manejin ɗan abin da suke samu da ɗimbin ƙalubalen rayuwa da na iyali da suke kokawa da su. Da fatan kafin wannan gwamnati ta kammala wa’adin ta za ta tabbatar ta duba batun nan da aka tayar cikin shekarar da ta gabata na daidaita albashin ma’aikata, domin ɗaga darajar waɗanda suke karɓar albashi mafi ƙaranci da wanda nasu albashin yake da tsoka.

Kamar yadda shugaba Buhari ya faɗa a cikin jawabin sa na sabuwar shekara ga ’yan Nijeriya, gwamnatin sa za ta mayar da hankali wajen amfani da fasahar sadarwa ta ICT domin samar da ayyukan yi ga matasa da buɗe ƙarin hanyoyin shigar kuɗaɗe asusun gwamnati. Lallai ya kamata gwamnati ta ba da muhimmanci sosai ba kawai ga harkar sadarwa ta ICT ba, har ma da sauran ɓangarorin gwamnati da ake fuskantar ƙarancin ma’aikata, musamman a harkar tsaro. Alhalin ga miliyoyin matasa nan sun gama makaranta suna neman ayyukan yi amma babu dama. An mayar da samun aikin yi sai mai uwa a gindin murhu.

Na yi imanin wannan gwamnati tana da kyakkyawar aniyar samar da cigaba da bunƙasa rayuwar ’yan Nijeriya, amma wajibin ta ne ta nuna wa ’yan Nijeriya cewa, kowanne vangare na da haƙƙin kula da matsalolin sa, da kuma ba shi dama kamar saura. Talakawa na bukatar su gani a ƙasa, daga kan hanyoyin su, kasuwannin su, asibitoci da makarantun ’ya’yan su, suna son su ga shaidar lallai wani abu na faruwa, ba kawai a labarai ba ko a sa su yi ta cike takardun, amma ba su da tabbacin yaushe abubuwan da ake ta alƙawarta musu za su isa gare su.

Muna fatan kamar yadda ubangiji ya ja kwanan mu muka ga wannan shekara cikin masu rai, Allah ya sa mu ga ƙarshen wannan shekara lafiya cikin farin ciki da ƙaruwar arziki. Allah ya kare mu, Ya kare rayuwar mu daga dukkanin wani sharri da ke cikin wannan shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *