2023: Na sanar da Buhari burina na neman shugabancin ƙasa, cewar Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta ba shi damar bayyana wa shugaban burinsa na neman tsayawa takarar Shugaban Ƙasa ya zuwa 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja jim kaɗan bayan ganawar sirri da ya yi da Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa, tare da cewa duk da dai ya sanar da Buhari aniyarsa amma zai ci gaba da tuntuɓa da neman shawarwarin ‘yan Nijeriya.

Tinubu ya yi watsi da batun cewa “mai zaɓen sarki ba zai iya zama sarki ba”, yana mai cewa zai so ya zama magajin Buhari a 2023 don ci gaba da kyawawan ayyukan jam’iyyar APC mai mulki.

Da yake yi wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya ce, “Na sanar da Buhari burina amma ban sanar da ‘yan Nijeriya ba tukuna, ina kan neman shawara, kuma ba ni da wata matsala a kan haka.

“Ban tsayar da adadin mutanen da zan tuntuɓa ba, za ku ji komai nan ba da daɗewa ba, abin da kuke so ku ji shi ne in fito fili in bayyana ƙudirina. Kun dai ji gaskiyar zance daga gare ni cewa na shaida wa Shugaba Buhari burina wanda ba ku buƙatar wasu amsoshi fiye da haka.”

Da aka nemi jin amsar da Buhari ya ba shi, Tinubu ya ce “Wannan lamarinmu, shi mai ra’ayin siyasa ne, bai ce mini in dakata kada in yunƙura don cimma burina ba. Don haka me zai sa in zaci fiye da haka daga gare shi?

“Kana tafiyar da tsarin dimokuraɗiyya, kuma dole ne ka yi amfani da ƙa’idoji da kyawawan ɗabi’u na dimokuraɗiyya, wannan shi ne.”

Sai dai, Tinubu ya ƙi bada zarafin tattaunawa da shi kan abin da ya shafi yaƙin neman zaɓen da aka ga wasu ƙungiyoyi na yi wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, SAN, da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi dangane da neman shugabancin ƙasa a 2023.

Inda ya ce, “Ba na buƙatar yin magana a kan wasu a yanzu, batuna zan tattauna. Ina da ƙwarin gwiwa da hangen nesa da ƙarfin da zan yi mulki don ɗorawa daga inda Shugaba Buhari zai tsaya don gyara Nijeriya…”