Ka yi murabus domin ceto Zamfara daga rugujewa – PDP Ga Matawalle

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta yi kira ga Gwamna Bello Mohammed Matawalle, da ya yi murabus daga muƙaminsa na gwamnan jihar da nufin ceto jihar daga durƙushewa baki ɗaya.

Jam’iyyar ta kuma bayyana jihar a matsayin koma baya duba da halin ko-in-kula da gwamna Bello Mohammed Matawalle yake yi wajen gudanar da mulkin jihar.

Mataimakin shugaban jam’iyyar Farfesa Kabiru Jabaka ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai a Gusau babban birnin jihar.

“Kowa ya san cewa Zamfara ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga da dama, sace-sacen mutane, biyan kuɗin fansa ga ‘yan bindiga, amma duk da haka gwamnan ya jajirce kan irin wahalar da mutanen karkara ke fama da su.

“Abin takaici ne yadda duk harkokin zamantakewa da tattalin arziki suka durƙushe ciki har da ayyukan noma da aka san jihar da su, “amma duk da haka gwamnan ya ji daɗin zuwa Jamhuriyar Nijar domin kallon gasar kokawa yayin da jihar ke ci da wuta a kullum ba tare da gwamnati ta damu ba.”

Jabaka ya ƙalubalanci cewa duk makarantun jihar Zamfara sun kasance a rufe har abada ba tare da sanin lokacin da za a buɗe su ba, duba da muhimmancin ilimi ga jihar.

Jigon na PDP ya ci gaba da ƙalubalantar hakan, ya ce tun farkon wannan gwamnatin ta Gwamna Bello Matawalle, ba zai iya yin alfahari da aikin babban birnin jihar ba wanda ke da tasiri kai tsaye ga talakawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *