Sojoji sun rufe kasuwar da ta zama cibiyar kasuwancin Boko Haram a Adamawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar sojojin Nijeriya ta rufe kasuwar shanu ta Song bayan bayanan sirri sun nuna cewa, ’yan Boko Haram na hada-hadar kasuwancinta a kasuwar.

Rufe kasuwar dai ya haifar da ce-ce-ku-ce, yayin da wasu ’yan kasuwar ke zargin matakin da sojoji suka ɗauka, bayan da suka ƙi amincewa da buƙatar sojojin da ke wurin na neman maƙudan kuɗaɗe domin su samu damar yin kasuwanci.

Wani ɗan kasuwa da ya zanta da manema labarai, ya ce, sojojin sun buƙaci ƙungiyar ’yan kasuwa da ke kula da kasuwar da ta ba su miliyoyin naira.

Amma Kwamandan Birgediya 23, Gibson Jalo Cantonment, Birgediya Janar Aminu Garba, ya ce an rufe kasuwar na wani ɗan lokaci ne domin duba ayyukan ’yan ta’adda.

Idan za a iya tunawa, a ranar 14 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, an ce sojoji sun rufe wata kasuwar mako-mako a garin Gombi, saboda fargabar harin Boko Haram.

Gombi dai na da iyaka da tsaunin Mandara wanda ‘yan Boko Haram suka saba amfani da su wajen kai hare-hare a ƙauyuka da kusa a yankin Askira Uba da ke ƙaramar hukumar Jihar Borno da kuma ƙananan hukumomin Michika, Madagali, Hong, da Gombi na Adamawa. .

Majiyoyin soji a lokacin sun yi ikirarin cewa, an rufe kasuwar Golongtabal da ke ƙaramar hukumar Gombi ne domin kaucewa kutsawa daga ƙungiyoyin ’yan ta’adda.

Rundunar sojin ta bayyana cewa, an ɗauki matakin ne domin daƙile hare-haren da a ke shirin kaiwa da kuma kare al’umma daga duk wata barazana da za ta iya fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *