An kama mutum shida kan zambar mutane a shafin masu auren jinsi a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan Sandan Jihar Nasarawa a Arewa ta Tsakiyar Nijeriya sun kama mutum shida da ake zargin suna amfani da wani shafin intanet suna zambar mutanen da suke auren jinsi ɗaya.

An ce waɗanda ake zargin suna amfani da shafin ne don neman amincewar mutane kafin daga bisani su zambace su.

Kamen ya zo ne bayan wani da abun ya shafa ya ce an ɗauki hotunan tsiraicinsa, kuma an yi masa barazanar yaɗa hotunan idan bai ba da kuɗi ba.

An ce lamarin ya faru ne a unguwar Masaƙa, a Ƙaramar Hukumar Karu da ke da iyaka da birnin tarayya Abuja.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Ramhan Nansel ya gaya wa manema labarai cewa wanda ake zargin, maza huɗu da mata biyu, sun yaɗa hotunan masu neman auren jinsi ɗaya, kuma sun gayyaci masu sha’awar yin haka don shirya ranakun da za su haɗu.

Sannan kuma sai su zambaci mutanen ko su ƙwace musu ƙadarorinsu kuma su yi musu barazanar ɓata musu suna don rufe bakinsu.

‘Yan sandan sun ce za a yanke wa waɗanda ake zargin hukunci bayan kammala bincike.

Gwamnatin Nijeriya ta hana auren jinsi ɗaya, ta kuma saka dokar ɗaure mutum har na shekaru 14 idan an kama masu aikata laifin.