An karrama mawallafin jaridun Manhaja, Blueprint a Kaduna

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Rotary da ke Kaduna, ta karrama mawallafin jaridun Manhaja da Blueprint kuma mamallakin tashar We FM da ke Abuja, Alhaji Mohammed Idris Malagi (Kaakaki Nupe), da lambar yabo.

Ƙungiyar ta karrama Alhaji Malagi ne saboda irn gudunmawarsa da ya bayar ga cigabanta.

An miƙa wa Kaaki Nupe lambar ne a Kaduna a wajen taron asusun neman tallafi don amfanin marasa galihu da miƙa kyaututtuka da ƙungiyar ta shirya.

A cewar Ƙungiyar, ta miƙa wa Alhaji Malagi lamabr ne domin nuna godiyarta dangane da gudunmawar da yake ba ta, da kuma ƙarfafa masa ci gaba da hakan.

Sa’ilin da take jawabi a wajen taron, Shugabar Ƙungiyar, Esther Gaya, ta ce sun shirya taron ne domin tara kuɗin da ƙungiyar za ta yi amfani da shi wajen tallafa wa mabuƙata da marasa galihu a cikin al’umma.