Ƙidaya: ‘Yan Nijeriya miliyan 250 na iya tsunduma cikin fatara, inji Majalisar Ɗinkin Duniya

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi iƙirarin cewa, aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 250 na iya tsintar kansu a cikin tsananin halin ƙaƙa-nikayi na fatara a nan gaba.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Gidauniyar Majalisar Ɗinkin Duniya Kan Yawan Jama’a (UNFPA) a Nijeriya a yayin da Wakiliyar Ƙasa ta Gidauniyar, Ulla Mueller, ke gabatar da jawabi a wajen taron bin ba’asi da Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta shirya kan ƙidayar jama’a da ƙasar za ta gudanar a 2023 a ɗakun taro na ƙasa da ƙasa dake Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua a Abuja, Babban Birnin Nijeriya ranar 21 ga Nuwamba, 2022.

Mueller ta ce, samun mafita kan wannan matsala sun haɗa da dole sai Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta aiwatar da tsare-tsaren da tuni aka amince da su a 2021 zuwa 2022, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ke tallafawa tare da wani kason kuɗi daga gwamnatin, don ganin an taimaka wa talakawan ƙasar, don ƙarfafa rayuwarsu.

Haka nan, sai al’ummar ƙasar sun rungumi tsarin iyali daidai gwargwadon yadda za su iya ɗaukar nauyin ‘ya’yan da su ke haifa ta fannin ba su ilimi, kula da lafiyarsu da sauransu.

Ta ƙara haske da cewa, wannan mataki zai fara ne tun daga lokacin da mace ta samu juna-biyu wajen kula da lafiyarta, abincinta har zuwa haihuwarta da rainon abinda ta haifa matuƙar a na so a kaucewa faɗa wa cikin tsananin fatara, idan aka dubi yadda yawan al’umma ke ƙaruwa cikin hanzari qa Nijeriya, musamman ma yankin Arewa.