Lokaci yana ƙure wa Nijeriya kan hatsarin yawan jama’a, inji Gidauniyar Bill Gates

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Gidauniyar Melinda and Bill Gates ta bayyana cewa, lokaci yana ƙure wa Tarayyar Nijeriya kan hatsarin da ta ke fuskanta game da yawan jama’a, idan aka yi la’akari da yadda cigaban ƙasar ke yin tafiyar hawainiya.

Gidauniyar ta bayyana hakan ne a wajen taron da Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta shirya ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, a, wanda aka gudanar ranar 21 ga Nuwamba,2022, a ɗakin taro na Shehu Musa Yar’Adua dake Abuja.

Daraktan Ƙasa a Nijeriya na Gidauniyar Gates, Jeremie Zoungrana, wanda ya aike da jawabin fatan alheri a wajen taron, ya ƙara da cewa, yawan jama’a da Nijeriya ke cigaba da samu bai zo daidai da yawan cigaban da ƙasar ke samu ba ta fuskokin tattalin arziki, lafiya, ilimi da sauran abubuwan bunƙasa, wanda hakan ne ke nuni da hatsarin da ƙasar ke fuskanta.

Ya ce, dole ne a samar da cigaba bisa la’akari da yawan jama’a ta hanyar tsara iyali gwargwadon cigaban ƙasa ko kuma tabbatar da cigaban gwargwadon bunƙasar Nijeriya tun kafin lokaci ya gama ƙure wa ƙasar.

Daga nan ya bayar da tabbacin Gidauniyar Melinda and Bill Gates wajen cimma wannan buri, kamar yadda ta saba yi.