Mahaifiyar ɗalibar Yauri da aka yi garkuwa da ita ta mutu saboda takaici

Daga WAKILINMU

Mahaifiyar ɗaya daga cikin ɗaliban Sakandiren Gwamnati a Yauri da aka yi garkuwa da su lokutan baya, ta rasu.

Majiyarmu ta ce, takaicin sanin ‘yarta na ɗauke da cikin masu garkuwar na daga cikin dalilan da suka yi ajalin matar.

Majiyar ta ƙara da cewa, ana kyautata zaton mahaifiyar ta kwanta dama ne saboda tsananin damuwa da ta shiga sakamakon cikin da ‘yan bindigar suka yi wa ‘yarta bayan da suka yi garkuwa da ita.

Yarinyar da lamarin ya shafa na ɗaya daga cikin ɗaliban makarantar su 11 da suka rage a hannun ‘yan bindigar daga cikin ɗalibai sama da 100 da aka sace a wancan lokaci.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa, mahaifiyar yarinyar ta yanke jiki ne ta faɗi bayan samun labarin ‘yan fashin dajin sun yi wa ‘yarta ciki.

A ranar 17 ga Yunin 2021 ‘yan ta’addan suka kai hari makarantar da ke Yauri a Birnin Kebbi, inda suka kwashi sama da ɗalibai 100 da malamai takwas tare da kashe ɗan sanda ɗaya.

Bayan wasu kwanaki da faruwar hakan, jami’an tsaro suka yi nasarar kuɓutar da wasu daga cikin ɗaliban da ma malaman, wasunsu kuma suka tsere da kansu.

Daga bisani, an sako malaman da wasu ɗalibai bayan da aka biya fansa.