An miƙa cibiyar wasannin motsa jiki da al’adu da Ƙasar Sin ta samarwa Tunisia

Daga CMG HAUSA

Rahotanni daga ƙasar Tunisia na cewa, an yi nasarar damƙa cibiyar wasanni da al’adun matasa ta Ben Arous da ƙasar Sin ta ba da taimako wajen samar da ita, a Arewa maso gabashin Tunisiya.

Jami’i mai kula da aikin gina cibiyar dake aiki a ma’aikatar kula da kayayyakin aikin ƙasar Nizar Zoghlami ne ya bayyana hakan a ranar Juma’ar da ta gabata, a wani bikin mika cibiyar da ya gudana a lardin Ben Arous.

Yana mai cewa, nan ba da jimawa ba, za a buɗe cibiyar ga jama’a wadda ake fatan za ta kuma kawo farin ciki ga ‘yan ƙasar Tunisiya.

Ya bayyana cewa, ma’aikatan ƙasar Sin sun shawo kan wahalhalu da suka kunno kai ba zato ba tsammani yayin aikin gina cibiyar, musamman a sakamakon tasirin annobar COVID-19.

Darektar sashen samar da ababen more rayuwa na ma’aikatar matasa da wasanni ta ƙasar Tunisia, Naoufel Bel Haj Rhouma, ta miƙa godiyar ma’aikatarsa ​​ga ɓangaren ƙasar Sin.

Rhouma ta ce, ma’aikatan gine-gine na ƙasar Sin, suna da aminci kuma sun kammala shirin a kan lokaci.

Mai fassara: Ibrahim