Bikin tsakiyar kaka na 2022 da CMG ya nuna ya samu yabo sosai daga masu kallo a gida da waje

Daga CMG HAUSA

A yammacin jiya Asabar 10 ga watan Satumba ne, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na ƙasar Sin (CMG) ya watsa shagulgunan bikin tsakiyar kaka na shekarar 2022 kai tsaye, inda Sinawa a sassan duniya suka kalli cikin farin ciki da annashuwa tare da iyalansu.

Mutane miliyan 238 a duk faɗin duniya suka kalla.

Ya zuwa misalin ƙarfe 10 na daren ranar 10 ga watan Satumba, agogon Beijing, adadin waɗanda suka kalli shirye-shiryen kai tsaye, ya kai mutane miliyan 238.

Kana yawan waɗanda suka karanta jigon bikin da abin shafa, sun zarta biliyan 7.7, yayin da adadin hotunan bidiyo da aka watsa game da bikin ta kafar intanet ya kai kimanin miliyan 900.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *