An kammala gasar bidiyo ta matasan Sin da Afrika ta “Great to meet you”

Daga CMG HAUSA

An kammala gasar bidiyo ta matasan Sin da Afrika ta “Great to Meet You” karo na farko jiya Asabar, gaba ɗaya bidiyo 102 ne suka shiga gasar, inda guda 3 suka samu kyautar matsayi na farko, guda 6 suka samu na biyu, saura goma suka samu na matsayi na uku.

An shirya bikin miƙa lambobin ne a hedkwatar babban rukunin gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin wato CMG na nahiyar Afirka dake birnin Nairobin ƙasar Kenya, tare kuma da gabatar da shirye-shirye kai tsaye ta kafar bidiyo a faɗin duniya.

Hedkwatar CMG dake Afirka ce ta shirya gasar tare da haɗin gwiwar makarantar koyon aikin yada labarai da al’adun ƙasa da ƙasa na jami’ar Zhejiang, inda suka gayyaci shugabannin manyan kafofin watsa labarai na ƙasashen Afirka da masanan kafofin watsa labarai na ƙasar Sin domin su tantance bidiyon da aka gabatar.

Babban taken gasar shi ne “Matasan Sin da Afirka su haɗa kai domin gina kyakkyawar makomar al’ummomin Sin da Afirka a sabon zamanin da muke ciki”, ana sa ran matasan Sin da Afirka, za su nuna makoma mai kyau ta haɗin gwiwar dake tsakanin sassan biyu ta hanyar ɗaukar faifan bidiyo.

Tun bayan da aka ƙaddamar da gasar a ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata, matasan Sin da Afirka waɗanda suke tsakanin shekaru 20 zuwa 40 sun nuna kwazo da himma wajen gabatar da faifan bidiyon da suka ɗauka, daga ƙasashen Najeriya da Kenya da Benin da Angola da Tanzaniya da Jibouti da Kamaru da Madagascar da Mauritius da Mozambick da sauransu.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa