An naɗa Arabo sabon Sakataren Ƙaramar Hukumar Lafiya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

An naɗa Alhaji Mohammed Haliru Arabo a matsayin sabon saktataren Ƙaramar Hukumar Lafiya, fadar gwamnatin jihar Nasarawa. 

A cikin wata sanarwa ta musamman ɗauke da sanya hannun shugaban Ƙaramar Hukumar Lafiya, Honorabul Aminu Mu’azu Maifata da aka bai wa wakilinmu kwafi, Honorabul Maifata ya bayyana sabon sakataren a matsayin mai ƙwazo da sanin ya kamata da kuma ƙwarewa. Shi ya sa a cewarsa mahukuntan ƙaramar hukumar suka yanke shawarar naɗa masa mukamin. 

Ya taya sabon sakataren murnar naɗin nasa, inda ya buƙace shi da ya yi aiki tuƙuru don cigaban ƙaramar hukumar Lafiya da jihar baki ɗaya don kwalliya ta biya kuɗin sabulu. 

Shi ma a nasa ɓangaren dayake zantawa da wakilinmu a ofishinsa dake ƙaramar hukumar daga bisani bayan naɗin nasa sabon sakataren, Alhaji Mohammed Haliru Arabo ya gode wa mahukuntan ƙaramar hukumar ta Lafiya ƙarƙashin jagorancin Alhaji Aminu Mu’azu Maifata dangane da wannan karamci da suka yi masa, inda ya yi alƙawari cewa ba zai ba su kunya ba. 

Ya kuma yaba wa shugaban ƙaramar hukumar wanda abokin takararsa ne a zaɓen fidda gwanin Jam’iyyar APC da ya gabata, inda ya ce ba shakka Honorabul Mu’azu Maifata mutum ne wanda ya san rayuwa ya kuma ƙware a harkar siyasa.

Har ila yau Alhaji Haliru Arabo ya alaƙanta ɗimbin nasarori da ƙaramar hukumar ta cimma kawo yanzu cewa sanadiyyar shugabanci nagari ne da Honorabu Aminu Maifata ke gudanarwa. 

Daga nan sai Alhaji Mohammed Haliru Arabo ya yi amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga magoya bayan Jam’iyyar APC a jihar da ƙasa baki ɗaya su tabbatar sun yi zaɓi nagari a lokacin zaɓukan gama-gari na shekarar 2023 dake tafe musamman su tabbatar sun zaɓi duka ‘yan takarar APC a duka matakai don basu damar samar musu da ribobin dimokaraɗiyya kamar yadde suka yi alkawari. 

Idan ba a manta ba sabon sakataren ƙaramar hukumar ta Lafiya wato Alhaji Mohammed Haliru Arabo ya ƙara da shugaban ƙaramar hukumar maici yanzu, Honorabu Maifata a zaɓen fidda gwanin Jam’iyyar APC, inda bayan Mu’azu ya yi nasara ya kuma naɗa Arabo a matsayin sakataren ƙaramar hukumar matakin da har yanzu masu ruwa da tsaki da sauran magoya bayan jam’iyyar a jihar ke cigaba da yabawa.