Jama’ar mazaɓar Tofa, Dawakin Tofa da Rimin Gado sun koka da jagorancin Tijjani Joɓe

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An ƙalubalanci ɗan majalisar Tarayyar mai wakiltar Ƙananan hukumomin Tofa, Dawakin Tofa da Rimin Gado a Majalisar Tarayya, Tijjani Abdulƙadir Joɓe da cewa tsawon lokaci da ya yi yana wakiltar yankin ba wani abu takamaimai na cigaban al’umma da ya kawo wa yankin.

Ɗaya daga cikin ‘yan Jam’iyyar NNPP Hon. Rabiu Abdullahi Rimin Gado ya bayyana hakan lokacin wata zantawa da ‘yan jarida a Kano.

 Ya ce kusan shekaru 16 ba wasu ayyukan raya ƙasa da yake yi, sannan ba wanda ya samar wa aiki ko ya ba shi wani wadataccen jari da zai gina kansu.

Don haka ya ce duk da ɗan majalisar shine aka sake tsayarwa ɗan takarar majalisa a jam’iyyar su ta NNPP za su zaɓi cancanta ne a kowace jam’iyya.

Tun kafin wannan dama akwai ‘yan yankin da dama da suke ƙalubalantar ɗan majalisar da cewa ba sa iya samunsa su gabatar masa da buƙatunsu amma ba sa iya samunsa su gabatar masa sannan kuma baya ɗaukar kiran waya balle ma su yi magana da shi akan buƙatun su.

Don haka suke ganin suna da buƙatar a samu sauyi na wakilcin da ake da zai riqa sauraren buƙatunsu da kawo musu ayyuka kamar yadda suke gani wasu ‘yan majalisun na yi.

Sai dai kan wannan mun tuntuɓi Daraktan yaqin neman zaɓe na ɗan majalisar Adamu Abubakar ta wayar hannu amma bai ɗauka ba, haka shi ma ɗan majalisar, Hon. Abdulƙadir Jove bai ɗauki waya ba bai kuma aiko da amsar saƙon kar ta kwana da muka tura masa ba akan lamarin har zuwa wannan lokaci.