Sarkin Fulanin Legas ya gudanar da taron zaman lafiya ga sarakunan Fulani

Daga DAUDA USMAN a Legas

Sarkin Fulanin Jihar Legas mai Martaba Dakta Mohammed Abubakar Bambado na II kuma shugaban Majalisar Sarakuna da Qungiyoyin Fulani a Nijeriya ya gudanar da taron sarakuna da sauran shuwagabannin ƙungiyoyin Fulani na ƙasar nan a Jihar Legas domin tattauna hanyoyin zaman lafiya a ƙasar nan.

Taron wanda ya gudana a harabar babban ofishin Sarkin Fulanin dake cikin garin Legas a ƙarshen makon da ya gabata, waɗanda suka samu halartar taron sun haɗa da Sarkin Fulanin Abeokuta kuma sakataren majalisar Alhaji Kabiru Labar da harɗon jihar Oyo, Alhaji Yakubu Bello da Alhaji Abubakar shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na Jihar Oyo da Alhaji Suleman Yakubu shugaban ƙungiyar Gam Allah Fulbe.

Sauran sun haɗa da Alhaji Aliyu Bambado, Galadiman Jihar Legas da Walin Shagamu da waɗansu sarakunan Fulani waɗanda suka fito daga jihohin Ekiti, Kwara, Ondo da Osun da makamantansu.

Manyan baƙi a wajen taron sun haɗa da Kwanturol na RTD kuma Kaigaman Fataskum da Sarkin Hausawan Festac Alhaji Mustapha Musa uban tafiya da sauransu.

Tun da farko dai bayan buɗe taron da addu’a aka ƙaddamar da Dakta Ahmed Isa Jimeta a matsayin Kakakin Majalisar na jihohin Kudu da Sarkin Hausawan Alaba Suru da sauransu.

Bayan tattauna lamuran da za su wanzar da zaman lafiya a Nijeriya, sai Sarkin Fulani Dakta Alhaji Mohammed Abubakar Bambado na II ya cigaba da yi wa Fulani da sauran jama’ar da suka samu halartar taron huɗuba, inda ya yi kira ga jama’ar da su kasance masu lura a lokacin da hada-hadar siyasar 2023 ke ƙara ƙaratowa.

Sarkin ya kuma yi kira ga dukkan al’umma mazauna Jihar Legas da ƙasa bakiɗaya su kasance sun mallaki katin zaɓensu don zaɓar shuwagabanni nagari da za su kawo wa ƙasar cigaba.

Kazalika ya kuma yi kira ga ‘yan uwansa Fulani da sauran al’ummar Arewacin Nijeriya mazauna Kudu da su cigaba da sauran ƙabilun ƙasar nan cikin lumana da ƙaunar juna.

Ya kuma gargaɗi manema labarai da masu amfani da yanar gizo wajen yaɗa labaran gaskiya ba yaɗa jita-jita ba.