Ana tuhumar wani ƙwara da lalata da mata ‘yan aikinsa a Jos

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Garin Jos ta fara sauraron tuhumar da ake yi wa wani ƙwara ɗan asalin Ƙasar Lebanon, wanda ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a Jihar Filato, bisa laifin tilasta wa wasu yara mata ƙanana da ke yi masa aikin gida, yana lalata da su.

A zaman da kotun ta yi a Jos, alƙalin kotun Mai Shari’a Dorcas Venenge Agashi wacce ta saurari tuhumar da ake yi wa wannan ƙwara a ƙarar da aka shigar ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya, an ba da belin wanda ake ƙarar bisa buƙatar lauyan wanda ake ƙarar, Alexander Igbu.

Sai dai Alƙalin ta gindaya wasu tsauraran sharuɗɗa da suka haɗa da tarar Naira miliyan ɗaya, da kawo mutane biyu mazauna Jos, ‘yan kasuwa da aka san wurarensu na kasuwanci, kuma suka mallaki wasu muhimman kadarori. 

Sannan zai miƙa fasfon shi na fita ƙ asashen waje, da hana masa duk wata tafiya da za ta fitar da shi daga Jos.

An tsayar da ranakun 18 da 19 na watan Oktoba don cigaba da sauraron wannan shari’a.