Fargabar matsalar tattalin arzikin Nijeriya

A makon da ya gabata, Bankin Duniya ya fitar da rahotonsa kan taɓarɓarewar tattalin arzikin Nijeriya. Rahoto a ƙarƙashin duba irin ci gaban da Nijeriya ta samu, Cibiyar Hada-hadar Kuɗi Ta Duniya ta bayyana cewa, taɓarɓarewar yanayin tattalin arzikin Nijeriya na ƙara jefa al’ummar ƙasar cikin wani hali.

Rahoton ya nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki ya zama annoba ga rayuwar ’yan Nijeriya wanda dole ne hukumomi su yi yaƙi da hakan. Haɓakar hauhawar farashin kayayyaki da ke fitowa daga yaƙin Yukren, Bankin ya ce, zai iya jefa qarin ‘yan Nijeriya miliyan ɗaya cikin matsanancin talauci.

Tabbas tashe-tashen hankulan da yaƙin ya haifar da hauhawar farashin man dizal, man jiragen sama da alkama. Yunƙurin da farashin man jiragen sama ya yi daga Naira 190 kacal a watan Janairun bana zuwa sama da Naira 700 a yanzu ya sa farashin jiragen sama ya wuce gona da iri. Hakazalika, man dizal da ake amfani da shi wajen sufuri da injinan masana’antu, ya yi tsalle daga farashin kusan Naira 224.9 a farkon shekarar nan zuwa Naira 800 a kowace lita, kuma akwai rahotannin cewa zai iya kaiwa Naira 1,500 kan lita ɗaya nan ba da jimawa ba. Hakazalika, hauhawar farashin alkama ya taimaka wajen hauhawar farashin kayan abinci, tare da sanya abinci wahalar shiga bakunan mutane da dama.

Kafin yaƙin Ukraine, lokacin da hauhawar farashin kaya a Nijeriya ya kasance ɗaya daga cikin mafi girma a duniya, Bankin ya yi hasashen cewa daga 2020 zuwa 2021, ‘yan Nijeriya kusan miliyan takwas ne za su shiga cikin matsanancin talauci a ƙasar.

Baki ɗaya, bankin duniya, ya ce, daga shekarar 2020 zuwa bana, ’yan Nijeriya miliyan 15 ne ake tsammanin za su shiga talauci, bisa la’akari da munanan manufofin gwamnatinmu.

A bayyane ya ke ga masu lura cewa, wannan tattalin arzikin yana cikin matsala don haka hauhawar farashin kaya da cututtukan ke ƙara ta’azzara. Hasashen hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya haura zuwa kashi 17.71 cikin 100 a watan Mayu, bisa hasashen da Bankin ya yi na kashi 15.5 cikin 100 na wannan shekara – wata alama ce da ke nuni da irin giɓin da tattalin arzikin ƙasar ya samu. Daga aikin noma zuwa masana’antu, matakin ayyukan da ake aiwatarwa a cikin tattalin arzikin ya kasance cikin mawuyacin hali. Misali a harkar noma, kusan an daina noma a wasu sassan ƙasar saboda ayyukan ’yan fashin daji da ’yan ta’adda da sauransu.

Matsalolin da aka lissafa a sama ba su ne kaɗai matsalolin da ke addabar tattalin arzikim ƙasar ba. Bayan haka, ɗaukacin al’umma na fuskantar wasu matsaloli ko ƙalubale. Matsalolin ƙasar nan shi ne yadda ake ganin babu wani abu da ake yi don gano bakin zaren matsalar, da ana tavuka wani abu, a haƙiƙanin gaskiya da za a shawo kan waɗannan matsaloli. Abin da kawai mu ke da shi daga ma’aikatun hukuma shi ne kuka daga jami’an gwamnati. Daga kokawar Ministan Lafiya kan yadda yawan al’ummar ƙasar ke kawo cikas ga ci gaba, sai yadda takwaransa mai kula da harkokin kuɗi, ke ƙorafin cewa ƙasar ba za ta iya biyan albashi ba sai ta ci bashi.

Koke-koke ba za su sanya abinci a bakunan mutane ba, kuma ba za su rage farashin kayayyakin da suka yi tashin gauron zabi ba. Lokacin da buƙatu ya zarce wadata, dole farashi zai tashi.

Lallai hauhawan farashi wata alaƙar tattalin arziki ce; don haka, idan wata qasa tana fuskantar irin wannan hauhawar farashin kayayyaki, yana nuna wani abu ba daidai ba ne ga tattalin arzikin. Za a iya magance wannan babbar matsala ta hanyar kyakkyawan shiri na aiki.

Babban dalilin wannan taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma raguwar jin daɗin jama’a za a iya danganta shi da rashin mayar da hankali ga waɗanda alhakin su ne sarrafa tsarin. Kowane tattalin arziki yana buƙatar kulawa; yana buƙatar a sarrafawa. Sai dai akwai kwararan hujjoji da ke nuna rashin mutunta tsarin mulki domin duk ’yan siyasa sun karkata akalarsu ga siyasa da kuma miqa mulki ga gwamnati mai zuwa. Ministoci, shugabannin ma’aikatu, da hukumomi a yanzu sun fi zama jami’an fage, yayin da suke yaqin neman ƙuri’u domin samun muƙamai a harkokin siyasa na gaba. Duk waɗannan ana yin su ne domin cutar da al’umma baki ɗaya.

Wannan jaridar ta yi imanin ya kamata gwamnati ta damu da halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki. A duk ƙasar da ake da irin wannan hauhawar farashin kayayyaki da matsalolin da ke da alaƙa da su, an rage jin daɗin jama’a. Don haka ya kamata gwamnati ta yi gaggawar yin wani abu na zahiri game da hakan.

Muna roƙonta da ta zage damtse kan aiki, ta nunawa ’yan Nijeriya cewa ita ce ke kula da tattalin arzikin ƙasa. Akwai abubuwa guda biyu da za a iya yi don kawar da duk wani taɓarɓarewar yanayin tattalin arzikin ‘yan Nijeriya.

Gwamnati na iya sakin wani ɓangare na tsare-tsaren hatsi na ƙasar a daidai wannan lokaci domin daƙile tashin farashin kayayyakin abinci. Haka kuma ya kamata gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su binciko yadda gwamnatocin da suka shuɗe a ƙasar nan suka yi a lokacin da aka fuskanci irin wannan ƙalubale. Hakanan za ta iya ayyana dokar ta-ɓaci kan tattalin arzikin da nufin tattara duk albarkatun da ake buƙata don tunkarar waɗannan ƙalubalen a gaba.

A yau, manyan bankuna a duk faɗin duniya suna cikin tashin hankali, suna ɗaukar matakan da ba a saba gani ba don magance wannan annoba ta hauhawar farashin kayayyaki da yaƙin Ukraine ya haifar. Daga Birtaniya zuwa Amurka, Turkiyya, da Brazil, manyan bankuna sun ƙara yawan kuɗin ruwa.

Babban bankin Nijeriya ma ya yi haka a kwanan baya inda ya ƙara kuɗin ruwa daga kashi 11.5 zuwa kashi 13 cikin ɗari. Amma yana buƙatar yin ƙari; dole ne ta fito da manufofin da za su magance hauhawar farashin kayayyaki ta la’akari da keɓantacciyar ƙasar. Dole ne a tuna cewa babban aikinsa shi ne tabbatar da farashin da daidaiton farashin canji. Wannan ya fito ƙarara a sashe na 2 (a) na dokar babban bankin Nijeriya, 2007.

To, me ya sa CBN ke nisantar wannan nauyi? Me ya sa ta karkata akalarta ga tallafin wutar lantarki, noma da sauransu? Ba aikin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba ne ya shawo kan hauhawar farashin kayayyaki? Wannan shi ne aikin babban bankin, yana aiki tare da sauran hukumomin gwamnati, ta fuskar daidaita manufofi.

Ya kamata kuma CBN ya sake duba yadda ake bai wa manoman shinkafa rance, ɓangaren samar da wutar lantarki da sauransu. To amma, idan waɗanda suka ci gajiyar kuɗin sun qi biya a yau, me bankin zai bayar gobe?

Dole ne CBN ta haɗa kai da dukkan awararru domin daqile faɗuwar Naira. Muna kuma roaon shugaban ƙasa da ya yi kira ga ƙungiyar tattalin arziki da su gaggauta yin aiki kan wannan lamarin. Tattalin arzikin ya taɓarɓare kuma dole ne dukkan hannaye su kasance a wuri guda don magance shi. Dole ne wanda zai lashe zaɓe a gaba a duba irin mawuyacin halin tattalin arziki.