An sace ‘yan Chana da kashe jami’an tsaro a Jihar Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wata mahaƙar ma’adinai a Jihar Neja, inda suka sace ma’aikata ‘yan ƙasar Chana aƙalla huɗu, tare da kashe jami’an tsaro aƙalla shida wazanda suka ƙunshi ‘yan sanda da sojoji da kuma ‘yan sintiri na bijilante.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bala Kuryas, wanda ya tabbatar wa manema labarai, ya ce tuni aka tura jami’ai domin ganowa tare da ceto waɗanda aka sace a wani yanki na Ƙaramar Hukumar Shiroro.

Sai dai kuma wata majiya ta shada wa BBC, cewa sojoji 4 da ‘yan sandan sintiri 4 da kuma ‘yan ƙungiyar sintiri biyu aka kashe a harin.

Ba a dai san takamaimai waɗanda suka kai harin ba, amma dama Jihar Neja, na ɗaya daga cikin jihohin Nijeriya da ke fama da matsalar tsaro ta ɓarayin daji masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.

Baya ga mayaqan ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi, waɗanda a wani lokacin kan haɗa kai da ‘yan bindiga masu satar mutane.

Jihar Neja da wasu jihohin a Arewacin Nijeriyar da suka haɗa da Zamfara da Nasarawa na da arzikin ma’adanai da suka haɗa da zinariya, abin da kan kai ‘yan ƙasar Chana aikin haƙarsu.