An yaba wa ƙoƙarin Gwamnan Jihar Kano wajen inganta fannin lafiya

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa mutum ne mai tausayi da ƙoƙarin kawar da matsalolin da suka dami al’umma musamman yana sa ido da kula da kishin taimakawa bunƙasa lafiyar al’umma.

Shugaban sashin kula da harhaɗa magunguna kuma jam’in hulɗa da jama’a na.Kano Medical Centre, Pharmacy Ammar Khalid Mustafa ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Ya ce Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf da taimakon Kwamishinan lafiya suna ɗaukar matakai da suka kamata domin ganin sun kyautata lafiyar al’ummar Jihar Kano a fannoni da dama.

Pharmacy Ammar Khalil Mustafa ya bayyana cewa an samar da “Kano Medical Centre” ne  domin tallafawa bunƙasa lafiyar al’ummar a ƙasar nan don rage ɗawainiya da ake na zuwa ƙasashen waje domin neman lafiya.

Ya ce cibiyar dake ƙarsashin “Chief Medical Director Dakta Abdullahi Bawa wanda asalin kafata   daraktan cibiyar Mista Hassan Hajjaj ne ya yi niyyar kafa wajen gwaje-gwajen cututtuka sai  wasu ‘yan uwa da suke da asibitoci a ƙasashen Labanon, Kanada da Amurka suka shawarce shi  akan ya kamata ya samar da cibiyar.

Ya ce an yi ginin cibiyar ne mai hawa biyar cikin ƙasa da shekara uku, yanzu haka ma a gini hawa na  ɗaya  aka soma gudanar da harkokin kula da marasa lafiya nan bada daɗewa ba za a cigaba da kula da marasa lafiya da soma yin tiyata a sauran sassan.

Pharmacy Ammar Khalil Mustafa ya yi nuni da cewa an kashe makuɗan kuɗi wajen samar da cibiyar da sanya kayan aiki na zamani har zuwa yanzu ana cigaba da kawo muhimman kayan aiki duk da kuwa  matsalar hauhawar farashin Dala tasa an samu tsaiko amma ana ƙoƙarin  saka kayayyaki da ake da buƙata.

Ya ce shugaban cibiyar Chairman Alhaji Ali Alhagi da Darakta Mista Hassan Hajjaij da  Babban Medical Darakta Dakta Abdullahi Bawa suna mutuƙar ƙoƙarin ganin an samu nasarar kula da lafiya mai inganci a cibiyar ga marasa lafiya ba sai an fita waje ba.

Cibiyar na da  ƙwarewa da ƙwararrun ma’aikata ‘yan Nijeriya da kuma baƙi da aka kawo daga waje suna kuma da kayan aiki musamman a ɓangaren “Laboratory “da “Radiology” suna da “MRI machine” da kuma” CTScan”  da suke aiki lokaci ɗaya don sauƙaƙawa likitoci gano cuta ba tare da tsaiko ba.

Pharmacy Ammar Mustapa ya yaba da da irin ƙoƙari da asibitocin gwamnati suke saboda  yawan marasa lafiya da suke karɓa da hakan ya sa suke yi wa likitocin yawa ga shi kuma suna da ƙarancin kayan aiki na zamani da hakan jawo jinkiri  wajen duba mara lafiya akan lokaci har sai ya galabaita.

Ya ce masu kula da lafiya ‘yan ƙasar nan likitoci da masu jinya suna da ƙwarewa sosai, wani lokacin ma idan ka fita waje ganin likita sai ka samu ɗan Nijeriya ne dai likitan.

Pharmacy Ammar Khalid Mustafa ya yi nuni da cewa sakamakon irin jinƙai da tausayi da taimako na Daraktan cibiyar Mista Hassan Hajjaij ana sauƙaƙawa marasa lafiya da suka zo, da  ba za su iya biyan kuɗin kula da rashin lafiyar da aka  kawo su ba ya sa ana yi musu ragin abinda ya kama daga kaso 30 ko 50 na kuɗin.

By ukarofi