An yi garkuwa da sirikar Mangal a Katsina

Daga FATUHU MUSTAPHA

Rahotannin da Manhaja ta samu daga jihar Katsina, sun nuna ‘yan bindiga sun sace sirikar hamshaƙin ɗan kasuwar nan Alhaji Dahiru Barau Mangal, a Katsina.

Majiyar Manhaja ta ce lamarin ya faru ne a daren Talata a yankin ƙaramar hukumar Matazu, inda ‘yan bindigar suka je suka ɗauki Hajiya Rabi.

Majiyar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce da misalin karfe 1 na daren Talata ‘yan bindigar suka shiga gari suka tafi kai tsaye zuwa gidan Hajiya Rabi suka ɗauke ta suka yi gaba ba tare da an san inda suka nufa ba.

Da ma dai kafin wannan lokaci, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da sirikin ɗanta Buhari Muntari a cikin garin Katsina, inji majiyar tamu.

Maigidan Hajiya Rabi, Alhaji Muntari, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *