EFCC ta kama ‘yan fashin intanet 9 a Minna

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), ta cafke wasu ‘yan fashin intanet su tara a Minna, babban birnin jihar Neja.

EFCC ta cafke waɗanda lamarin ya shafa ne a ranar Litinin biyo bayan bayanan sirri da ta ce ta samu a kansu dangane da ayyukan zambatar mutane da suke aikatawa.

Kayayyakin da EFCC ta ce ta ƙwace a hannu matasan sun haɗa da ƙananan kwamfutoci da wayoyin salula da kuma motoci.

Hukumar ta ce, za ta gurfanar da ‘yan fashin a kotu da zarar ta kammala bincikenta.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*