An yi wa kwamishina kisan gilla a Katsina 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu, waɗanda a ke kyautata zaton ’yan bindiga ne, sun halaka Kwamshinan Kimiyya da Fasaha na Jihar Katsina, Malam Rabe Nasir, jiya Alhamis da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Manhaja ta kalato cewar, an kashe kwamishinan ne a gidansa da ke rukunin gidaje na Fatima Shema a cikin Birnin Katsina.

Majiyar ta ce, an kashe shi ne tun a ranar Laraba, inda ya yi kwanan keso, yayin da wata majiyar kuma ta ce, sai a ranar Alhamis aka kashe shi ɗin.

Wani abokin mamacin ya ce, “an harbe Marigayi Nasir ne bayan sallar la’asar a nan gidansa da ke Fatima Shema.”

Amma da Manhaja ta ziyarci gidan mamacin, inda ya tarar da wani mutum da ke jimamin mutuwarsa, ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun same shi a ɗakinsa, inda suka daɓa masa makami a cikinsa kuma daga bisani aka ja gangar jikinsa zuwa banɗaki aka rufe. 

“An caka ma sa makami, kuma aka tura gangar jikin banɗaki aka kulle,” inji majiyar.

Marigayi Rabe Nasir shi ne mai bai wa Gwamna Aminu Bello Masari shawara kan abin da ya shafi Kimiyya da Fasaha, kafin daga bisani a naɗa shi kwamishina. An haife shi ne a garin Mani a cikin Ƙaramar Hukumar Mani da ke Jihar Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *