Minista mai nakasa ne zai taimake mu

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Idan an duba kalmar nakasa, ta na nufin wani abu da ya gaza a jikin mutum ko wata halitta da ta ke buƙatar wani tallafi, don gudanar da rayuwa kamar sauran masu wadatar lafiya. Wanda ya rasa ƙafa, hannu ko uwa uba idanu ya na ajin masu nakasa. Kafafen labaru sun yi yunƙurin rage kaifin Kalmar ‘nakasa’ don kar ta zama kamar nuna wariya ko cin zarafi ga masu lalurar rashin wata gaɓa a jikinsu. Ba mamaki za ku karanta sassa daban-daban a kafafen labaru inda a kan rubuta ‘mutane masu buƙata ta musamman’ idan ana magana kan nakasassu.

An wanzar da wannan tsari tuni kan masu fama da cutar ƙanjamau da har kirari ake yi ma ta da lahira salamu alaikum zuwa cuta mai karya garkuwar jiki. Duk wannan don kaucewa cin zarafi ne ko jefa muguwar magana kan masu cutar. Mu kan ga nakasassu na fama da jidalin rayuwa ko ma wasu da dama sun duƙufa kan sana’ar bara da ambata ‘Allah ya ba ku mu samu’ da ya zama ba daɗin ji tun da duk wanda Allah ya halitta ai ba shi da shamaki wajen buƙatar Allah ya ba shi ba sai ya jira an ba wa wani sannan ya samu na sa rabon ba.

In an faɗaɗa ajin masu nakasa za a ga hatta kurame, bebaye, zabiya da sauransu na da buƙata ta musamman don haka sun shiga ajin masu buƙata ta musamman. Abin da kan kange mai nakasa daga shiga ƙungiyar masu buƙata ta musamman, sai don gatan sa da ko ya samu aikin yi ko an tara ma sa dukiya ya gada daga mahaifansa. Haƙiƙa nakasa ba ta na nuna wanda ya samu kan sa a cikin ta ya gaza ba ne wato ma’ana nakasa ba kasawa ba ne, mai nakasa ka iya rayuwa mai kyau daidai gwargwado ko ba zai kai ga morewa kamar sauran lafiyaiyu ba, to zan iya cin moriya ta dogaro da kan sa da biyan buƙatun rayuwarsa ba tare da kame-kame ko miƙa ƙoƙon bara don wani ya jefa ma sa taro da sisi ba.

Duk wannan shimfiɗa ce ta wannan darasi da na ke son bayani a kai don yadda a ka daɗe ana tattaunawa kan batun nakasassu kama daga gwagwarmayar samun dokokin da za su kare su har zuwa ga batun ɗaukar su aiki da kafa hukumomi ko ma’aikatu na musamman don kulawa da ajin waɗannan mutane da yawansu ya kai miliyoyi a cikin al’umma. Ƙungiyoyin nakasassu na bayyana cewa su na kaɗa ƙuri’a a lokacin zave kuma yawan su ya kai su iya samar da canji a turbar dimokraɗiyya amma tamkar ba su faye dacewa ba ne da samun waɗanda za su taimaka mu su. Wanann ya kai su ga yanke matsayar sai an samu mai buƙata ta musamman ya dare karagar mulki ko an naɗa shi babban mukami sannan za su samu wakilici mai inganci a gwamnati.

Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar nakasassu na Nijeriya Abdullahi Aliyu Usman ya ce, su na buƙatar gwamnati ta naɗa mu su minista mai nakasa bayan ƙirƙiro mu su ma’aikatar nakasassu. Wannan ya nuna naɗa mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan nakasassu da kafa hukumar kula da nakasassu ƙarƙashin ma’aikatar jinƙai bai wadatar ba. Abun lura shugaban hukumar nakasassun James David Lalu ma mai nakasar rashin ji ne da kunne sai an taimaka ma sa da masu fassara magana ta hanyar ishara sannan ya fahimata.

Abdullahi Usman ya ce, yin hakan zai taimaka ainun wajen sauya yanayin da masu nakasa su ke ciki na takaici maimakon a ce za a riƙa ɗibar kuɗin gwamnati a shekara a na raba mu su buhun shinkafa da yaduka da zannuwa idan an ba mu shinakafa in mun cinye yaya za mu yi kenan a ina za mu samu wasu buhunan, idan an ba mu yadi mun ɗinka in ya tsufa fa, shin tsirara za mu riƙa zama?, gaskiya mu na buƙatar a koya ma na yadda a ke kama kifi ne ba yadda a ke cin kifi ba.

Jagoran nakasassun na magana ne a bikin ranar nakasassu ta duniya ta bana da ke da taken ‘shigar da nakasassu lamuran shugabanci bayan annobar Korona’. Duk ranar 4 ga watan Disambar kowace shekara majalisar ɗinkin duniya ta ware ta don bita kan rayuwar nakasassu. Gwamnatoci da ƙungiyoyi a faɗin duniya na amfani da wannan lokaci wajen tattaunawa kan rayuwar masu nakasa don samu ƙarin hanyoyin inganta rayuwarsu. Wannan ya haɗa da tabbatar da samun daidaito ta hanyar guraben ayyukan yi, ilimi, muhalli, sutura da kiwon lafiya. Mallam Usman ya ba da wani labara mai ban takaici inda ya ce, iyayen wani yaro da ya samu hatsari a ka yankewa kafa sai su ka samo ƙoƙon bara su ka damƙa wa yaron wai ya zama Allah Sarki don haka ba wata moriya da za a yi da shi sai dai ya shiga bara kan tituna.

Hakanan ya kawo wani misalin na wasu yara biyu masu nakasa da ya gani a bakin kasuwa a Kebbi, ya tambaye su inda iyayensu suke suka bayyana cewa, suna a awaje kaza a cikin kasuwa, ya shiga cikin kasuwar ya same su, ya nemi yi musu nasihar rashin dacewar barin yara ƙanana su yi bara, sai suka ce masa ai ya zama wajibi yaransu su yi bara tun da aka halicce su da nakasa. Iyayen yaran don tsabar jahilci suka ƙara da cewa, ko da an hana yaran bara a nan duniya, a ranar lahira dole sai sun yi bara.

Wannan ya ba wa shugaban na nakasassu takaici inda ya yi amfani da misalin wajen buƙatar malaman addini su ƙara dagewa wajen wayarwa irin waɗannan mutanen kai kan mummunar fahimtar da su ka yi wa mutane masu nakasa. Don ai za a iya koyawa mai nakasa sana’a kuma ya zauna waje ɗaya ya ba da gagarumar gudunmawa ga al’umma. Ni na san wani mai nakasa da na haɗa takalma masu kyau da sarrafa fata ta hanyoyi masu ban sha’awa. Akwai makanikin babur da na sani ƙwarerre a Gombe wanda gurgu ne amma bai kashe zuciyarsa wajen bara ba. Irin wannan ma za ka taras ya kan taimakawa masu cikakkiyar lafiya.

Irin kuɗin da gwamnati kan ware don lamunin noma ko kiwo da sauran su, ya dace a duba ware maƙudan kuɗi wajen buɗe sana’o’i da za a riqa koyawa masu nakasa sana’o’i a dukkan jihohin Nijeriya, Bayan sun kammala kwarewa sai a samar mu su jari don zama masu dogaro da kai. Wannan hanya ce sadidan ta magance barace-barace.

Usaman ya ce, a kan wakilta mutane marar sa wata nakasa a jikin su a matsayin masu kare muradun nakasassu da hakan ba ya biyan buƙata.

Hakanan ya ce, nakasassu na buƙatar a ilmantar da su da ɗaukar su ayyukan yi da ma ba su wadataccen jari don gudanar da sana’a, da hakan ne sahihiyar hanyar hana bara. Ko da masu nakasa ba su shiga bara ba, z aka taras ba a ware ko tsara yanayi mai kyau da za su iya rayuwa daidai da sauran mutane ba, wato za ka ga a gine-gine da dama ba a tanadin yadda masu nakasa za su iya wucewa ba tare da da jagora ba.

Hakanan wajen tsallake tituna, shiga dakunan karatu, hawa dogayen benaye da sauran su. Lokaci ya yi da duk jama’a za su farka don kula da ’yan uwa masu nakasa don su ɗin ma ‘yan adam ne kuma dangin wane da wance. Wani ma ba da nakasar a ka haife shi samu ya yi wa imma ta rashin lafiya ko wani hatsari da ya rutsa da shi. Masu azancin magana kan ce matuƙar mutum na raye ba a gama yi masa halitta ba, wato ƙaddara ta kan iya faruwa ta iya sauya halittar mutum ya sauka daga ajin masu cikakkiyar halitta zuwa ta masu nakasa. Don haka aƙalla yana da kyau mutane masu lafiya su riƙa nuna tausayawa ga masu nakasa. Idan mai nakasa na bara to ko ba a ba shi kyauta ba, to kar a tsangwame shi, aƙalla a faɗa masa kalma mai daɗi ko da Allah ya ba da sa’a ne.

Wani sashen na al’umma da ke buƙatar kulawa ta musamman shi ne na marayu waɗanda ba su da gata ga kuma yanda tattalin arziki ya sa hatta yara masu iyaye ma ba lalle ne su na samun dukkan abubuwan da su ke buƙata na rayuwa ba. Hakan darasi na kowa ya duba hagu da daman a makwantan sa don gano inda marayu su ke don tallafa mu su ko da da kwanon ɗaya ne na abinci, abin sha da tufafi.

Gaskiya in mutane za su dau ɗabi’ar taimakawa juna ta kowane ɓangare, rashin jituwa ko zaman lafiya zai ragu ainun kuma albarka za ta iya dawowa irin ta zamanin kaka da kakanni. Wasu fa ɗan abin da su ke nema don biyan buƙatunsu bai taka kara ya karya ba. Naira 200-500 ta isa sanya wasu iyalan tsalle don murnar samun abun da za su ƙara wa miyarsu gishiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *