Matsalar tsaro: Buhari ya tura tawaga ta musamman zuwa Sakkwato da Katsina

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tura tawaga ta musamman da ta ƙunshi manyan jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Major General Babagana Monguno (Rtd), zuwa jihohin Sakkwato da Katsina domin duba ayyukan ‘yan fashin daji da suka ta’azzara a jihohin biyu.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da Babban Sufeton ‘Yan Sanda, Usman Alkali Baba da Daraktan Hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi da Darkata-Janar na Cibiyar Tattara Bayanan Sirri, Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar da kuma Major General Samuel Adebayo.

Cikin sanarwar da aka wallafa a shafinsa na facebook a yau Juma’a, Buhari ya ce, “Ina sa ran samun rahoton gaggawa da kuma shawarwari daga gare su game da matakan da suka dace in ɗauka don magance matsalar da ko shakka babu ta zama damuwa.”

Buhari ya ƙara da cewa, “Za mu yi dukkan abin da ya dace domin tabbatar da tsaron rayukan ‘yan Nijeriya a ko’ina suke a faɗin ƙasa. Za mu samar da dukkan abin da ake buƙata har sai a cimma cikakkiyar nasara.”

Sakkwato da Katsina na daga cikin sassan Nijeriya da ke fama da matsananciyar matsalar tsaro, wanda ko a baya-bayan nan sai da ‘yan ta’addan suka tare, tare da ƙona wata motar kasuwa gami da fasinjojin da ke cikinta a Sakkwato, kana suka yi wa wani kwashina kisan gilla a Katsina.

Tura tawagar da Buhari ya yi na zuwa ne a daidai lokacin da aka ga wasu ‘yan Arewa musamman matasa, suka soma gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda sha’anin tsaro ke daɗa taɓarɓarewa a Arewacin Nijeriya.