APC a Zamfara ba za ta yi nasara ba idan babu Sanata Marafa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

An jaddada cewa jam’iyyar All Progressive Congress APC a Jihar Zamfara ba za ta iya yin nasara ba idan babu Sanata Kabir Garba Marafa a zaɓukan shekarar 2027 mai zuwa.

Shugaban ƙungiyar Sanata Marafa Solidarity Movement a Jihar Zamfara, Muhammad M. Muhammad ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Gusau yau Juma’a.

A cewar sa wanzuwar jam’iyyar APC a Zamfara na da nasaba da jajircewar Sanata Kabiru Garba Marafa.

A cewar shi, ɗorewar Jam’iyyar APC a Jihar ba tare da Sanata marafa ba yana iya zama babban ƙalubale da ka iya haifar da faɗuwar jam’iyyar a jihar mai zuwa.

Ya yaba da salon shugabancin Sanata Marafa, inda ya ce ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen faɗin rashin adalcin da ake yiwa Sanata Marafa ba a jam’iyyance a jihar ta Zamfara.

Ya ƙalubalanci shugabancin jam’iyyar APC a Zamfara a kan biyan buƙatun wasu mutane biyu da kuma yin watsi da manyan shugabanni jam’iyyar irin su Sanata Marafa.

Ya bayyana shugaban na yanzu Hon. Tukur Danfulani a matsayin shugaban da bai cancanta ba wanda ya yana shugabancin Jam’iyyar karkashin bin umarnin wasu mutum biyu ne kawai don biyan buƙatar kanshi ba jam’iyyar APC ke gaban shi ba.

A cewar sa Alh. Surajo Garba maikatako ne kawai zai shugabanci jam’iyyar da zai iya magance rikicin jam’iyyar APC a jihar idan ya zama shugaban jam’iyyar a jihar.

“Idan Alhaji Surajo Maikatako ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar APC a jihar Zamfara, duk dan jam’iyyar za a yi masa adalci kuma Sanata Marafa ba zai bari Maikatako ya fifita shi ba ko kuma ya zama rakumi da akala. Yace

By ukarofi