Tsarin karatun sakandare: Ba a soke JSS da SSS ba, inji Ministan Ilimi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Maruf Alausa ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta soke tsarin karatun ƙaramar sakandare ta JSS da babbar ba, wato SSS, ko kuma maye gurbinsu da karatun shekaru 12 ga ɗalibai.

A yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja bayan taro na Musamman na Majalisar Zartarwa ta Ilimi (FCE) na 2025, ya ce Ma’aikatar ta miƙa buƙatar sauya tsarin ne zuwa zangon shekaru 12 tare da cigaba da bin tsarin 6-3-3-4.

Ya ce yana da muhimmanci a koma wa tsarin 12-4 daga 6-3-3-4 wanda zai taimaka wajen samar da nagartattun ɗalibai.

Ministan ya kuma ce tsarin 12-4 shi ne manyan ƙasashen da suka ci-gaba ke amfani da shi, waɗanda suka haɗa da Birtaniya da Brazil da kuma Ghana a nan Afirka.

Ya ƙara da cewa, a watan Oktoban 2025 ne za su samu sakamakon buƙatar a yayin zaman FCE, ya na mai cewa ba abu bane da za a aiwatar da shi nan da nan ba.

Hakan na zuwa ne a lokacin da wasu rahotanni suka yi ta yaɗa cewa an soke tsarin karatun JSS da SSS a makarantun sakandare a Nijeriya.

Kazalika, ya ce Gwamantin Tarayya za ta cigaba da ƙoƙarin samar da tsare-tsaren da za su inganta harkokin ilimi a Nijeriya domin amfanin ƙasa da al’ummarta.

By Babaji