APC ta yi wa PDP ba-zata a Jigawa ta Gabas

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

Jam’iyyar APC mai mulki ta yi nasarar lashe kujerar sanata da ta majalisar wakilai a yankin Jigawa ta Gabas.

Yauin zaɓen da ya gudana ranar Asabar, ɗan takarar APC, Ahmed Abdul Hamid Malam Madori, ya samu nasara da ƙuri’u 136,977.

Inda ɗan takarar jam’iyyar NNPP, Muhd Garba ya zamo na biyu da ƙuri’a 29,485, sannan Dr. Nuruddeen Muhammad na PDP ya sami ƙuri’a 107,457.

Baturen zaɓen, Farfesa Adamu Usman Isge, shi ne ya sanar da hakan inda ya bayyana Ahmed Abdul Hamid a matsayin wanda ya yi nasara.

A ɓangaren majalissar wakilan Hadejia, Auyo da Kafin Hausa ɗan majalisar mai ci Usman Ibrahim Kanfanin shine ya yi nasara da ƙuri’a 56,891.

Sai ɗan takarar jam’iyyar NNPP Baffa Sale ya sami ƙuri’a 10,7891 inda ɗan takarar jam’iyyar SDP, Suleiman Isah Sidi ya tashi da ƙuri’a 40,628.